24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Kotu ta yanke wa malamin makaranta hukuncin kisa bayan ya ɗirkawa ɗalibai 8 ciki

LabaraiLabaran DuniyaKotu ta yanke wa malamin makaranta hukuncin kisa bayan ya ɗirkawa ɗalibai 8 ciki

Kotu ta yanke wa wani malamin ƙasar Indonesia hukuncin kisa bayan an kama shi da laifin yi wa ɗalibai 13 fyade a makarantar kwana ta Islamiyya, wanda kuma a kalla takwas daga cikin waɗanda abin ya shafa sun samu ciki, a ranar Litinin din da ta gabata.

Kotun ta yankewa Herry Wirawan mai shekaru 36 hukuncin ɗaurin rai da rai a cikin watan Fabrairu, a shari’ar da ta ja hankalin al’ummar ƙasar kan cin zarafin mata a makarantun addini na ƙasar.

Kotu ta yanke wa malamin makaranta hukuncin kisa bayan ya ɗirkawa ɗalibai 8 ciki
Kotu ta yanke wa malamin makaranta hukuncin kisa bayan ya ɗirkawa ɗalibai 8 ciki

“Mun amince da ƙarar da masu gabatar da ƙara suka yi,” in ji sanarwar alƙali, wacce aka buga ranar Litinin a gidan yanar gizon babbar kotun da ke Bandung, lardin yammacin Java.

“A nan mun yankewa wanda ake tuhuma hukuncin kisa.”

Wirawan ba ya gaban kotu don daukaka karar, kamar yadda mai magana da yawun ya shaidawa AFP.

Indonesiya ta dakatar da aiwatar da hukuncin kisa na shekaru da yawa kuma an yanke hukuncin kisa na ƙarshe a cikin 2016.

Halin cin zarafin Wirawan a makarantar, shi ma a Bandung, ya fito fili ne a lokacin da dangin wata daliba suka kai ƙarar sa ga ‘yan sanda bisa laifin yi wa ‘yarsu fyade har aka samu ciki a bara.

A lokacin shari’ar da ya yi a baya, an bayyana Wirawan ya yi wa daliban mata fyaɗe da yawa daga iyalai marasa galihu kuma suna zuwa makarantar a kan tallafin karatu tsawon shekaru biyar. Ya kuma yi musu ciki a kalla takwas.

A gaban ƙaramar kotun, wanda ake tuhuma ya nemi alkali da ya yi masa sassauci, yana mai cewa yana so ya kasance a kusa don rainon yaransa.

Wani ɗan uwan ​​ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, hukuncin na ranar Litinin ya kawo adalci ga waɗanda lamarin ya shafa.

Hidmat Dijaya, kawun daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya ce “Da farko muna son a hukunta shi a gidan yari da kuma horo mai tsanani domin ya ji zafin laifin da ya aikata.”

“Amma, har yanzu muna jin hukuncin kisa ya bayyana wakiltar adalci.”

Lamarin dai ya jawo ɓacin rai na ƙasa da kuma ƙarin matsin lamba kan majalisar dokokin ƙasar don amincewa da wani ƙudurin doka da aka daɗe kan “kawar da cin zarafin mata” , da ke neman yaƙi da laifukan jima’i da kuma samar da adalci ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da batun fyaɗen aure.

Har ila yau shari’ar fyaɗe ta Bandung ta yi ƙarin haske kan matsalar cin zarafin mata a tsarin ilimin ƙasar Indonesiya, inda kashi 14 daga cikin 18 da aka gabatar wa hukumar kare haƙƙin yara a bara sun faru a makarantun kwana na Islama.

Ƙasar na da makarantun allo sama da 25,000 na Islamiyya, inda ɗalibai kusan miliyan biyar ke zaune da karatu a gidajensu.

Kotu ta yi watsi da ƙudirin gwamnatin Faransa na rufe wani masallaci

Wata kotun kasar Faransa ta rushe kudirin gwamnatin kasar na rufe wani masallaci da ke a birnin Bordeaux. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lauyan kungiyar masallacin Al Farouk, Sefen Guez Guez, a ranar Laraba ya ce kotun Bordeaux Administrative ta yi watsi da kudirin gwamnatin na ranar 14 ga watan Maris na rufe masallacin har tsawon watanni 6.

Anyi maraba da hukuncin

Ya lurar da cewa hukuncin kotun wani babban cigaba ne akan yadda gwamnati ta ke rufe masallatai ba bisa ƙa’ida ba. Ya kara da cewa masallacin yana zama a matsayin wurin haɗuwar musulmai.

An rufe masallacin Al Farouk da ke yankin Pessac kusa da garin Bordeaux bisa zargin shi da kare musuluncin tsageranci da kuma yada akidar salafanci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe