An kira Cosmas Korir a waya ne, inda aka shaida masa cewa yaci (Ksh) wato kudin kasar Kenya miliyan dari biyu da takwas 208m , wanda yayi daidai da Nairar Nageriya miliyan dari bakwai da hamsin da dubu dari biyar da casain da daya, da dari bakwai da goma N755, 591, 710
Ya karkata kudaden zuwa halattaccen kasuwanci, inda ya dinga siyawa kansa gidaje, da filaye.
Cosmas din ya siyawa matarsa uwar yayan sa wani dankareren Otal, domin ya bunkasa tattalin arzikin ta.
Kiran wayar da ya sauya rayuwar Cosmas har abada

Tsohon dan takarar majalisa daga yankin Pokot ta yamma, a kasar Kenya, Cosmas Korir, ya tuna wani kiran waya cikin marari, wanda ya canja rayuwar sa har abada.
Kiran waya ne wanda mutane kadan ne suke samun irin sa a rayuwar su, kiran da aka shaida masa cewa shine wanda ya lashe zunzurutun kudi har kimanin Ksh 208,733,619 wanda a kimar kudin Najeriya ya kama, Naira 755,591, 710
Da yake magana a gidan talabijin na Gamblers Paradise, Cosmas din yace, koda yaushe gidan yana cin nasara, kuma ya bayyana cewa yana tuki ne yayin da kyakkyawan labarin ya sameshi.
A fadar sa, yace zakwadin da yake yi, ya sha kansa ta yadda hatta abinci ma dandanon sa ya bambanta.

“Na dan zauna a kan ciyayi na dan lokaci, har saida na kusa dani suka dinga tambaya ko da gaskene “
Siyayyar da Cosmas yayi ta burga da kece raini
Saukar kudin ke da wuya cikin asusun sa, sai ya shiga katafaren shagon siyayya inda ya fito da wata dankareriyar mota kirar Toyota Landcruiser V8.
“Na sameta akan kudin Ksh miliyan 12m daidai da kudi Najeriya 43,438, 620 “take na bada kudin ta kuma har yau tana yi mini abin da nake so, babu maganar bashi”.
Ya kara da cewa, tsawon lokaci, ya na zagayawa tare da shawarar me ya kamata yayi da wadannan makuda kudade.
Kasantuwar ya taso a rubabben gida, Cosmas ya ware Ksh miliyan biyu 2m, domin gina gidan da zai zauna a kauyen su.
Saka hannun jarin gidaje
Ana cikin haka, sai wani aikin sa ya gaya masa cewa akwai wasu gidaje da aka sanya a kasuwa, a yankin Kitengela, a kan kudi Ksh miliyan hamsin 50m daidai da Nairar Nageriya miliyan dari da tamanin N180m, nan da nan kuwa ya sayesu ya zama mallakar sa.
Bayan wata guda, sai na fara karbar kudin haya Ksh 400,000 daidai da kudin Najeriya 1,400,000. Kamar yadda ya bayyana
Da yaji dadin wannan jari da ya sanya, sai ya sake sayen wani gidan na Ksh 62m daidai da Nairar Nageriya N224m wanda yake kawo masa kudin haya Ksh 500,000 duk wata.
Cosmas, ya siyawa matarsa wani dankareren Otal a garin Eldoret, abin da tuni ya bunkasa arzikin ta, shi ma kuma yanzu haka yana gina nasa otal din a wani fili na da ya mallaka.
Cosmas ya kara da cewa, mutane da yawa suna ta kiran sa a waya mafi yawa ma bai san su ba, kawai suna so ne su kulla abota da shi. Suna takura masa ta yadda har sai ya kashe wayar sa.
Hakan yasa ana ta kawo min dimbin bukatu, wadanda bai zama dole na iya biyan su ba, wannan ya sa wasu sunyi zucuya da ni.
“”Idan banda wannan cacar da na ci, da tuni yau ba anan nake ba, mai yiwuwa ina can a Bomet”.
Cosmas din ya fada.
Ficik! Ta fincike wa makwabciyarta kunne daya su na tsaka da ba hammata iska
Matar aure ta cire wa makwabciyar ta kunne daya. Yayin da Nwunye Ofo mai yara 4 da makwabciyarta Ogechi su ke tsaka da kwasar dambe akan leda, Ofo ta yi gaggawar dadumar kam Ogechi da kaifafan hakoranta ta cizge mata kunne daya.
Lamarin ya auku ne a wani gida da ke layin Agulese Ugwueme a Akwuke da ke karamar hukumar Enugu ta Kudu a jihar Enugu.
The Punch ta ruwaito yadda dama makwabtan ba sa ga maciji da juna saboda hayaniyar da kan hautsine tsakanin yaransu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com