35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

An tsinci gawar wani mutum dan shekara 55 a kan titi bayan ya bar gida zuwa cin kasuwa a jihar Jigawa

LabaraiAn tsinci gawar wani mutum dan shekara 55 a kan titi bayan ya bar gida zuwa cin kasuwa a jihar Jigawa

Wasu jami’an hukumar rundunar kiyaye farar hula, (civil defence ) sun gano gawar wani mutum,Isyaku Shuaibu, a karamar hukumar Kiyawa, dake jihar Jigawa. 


Jami’in hulda da jama’a na hukumar Adamu Shehu, a wani jawabi da fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe 9:30 na safe. 

gawar dattijo
An tsinci gawar wani mutum dan shekara 55 a kan titi bayan ya bar gida zuwa cin kasuwa a jihar Jigawa

Yadda aka gano gawar mamacin


Shehun yace, hukumar ta sami kiran gaggawa ne, inda aka nemi takai dauki da jami’an lafiya wurin da lamarin ya faru. 


“Da zuwan mu, sai muka iske gawar Shuaibu a gefen titin Kiyawa zuwa Andaza, kimanin nisan kilomita 2 daga garin Andaza. 


“Bayan an yi yan gwaje-gwaje a wurin, babu wata alamar rauni a jikin sa, daga nan sai aka garzaya da gawar sa zuwa asibitin Dutse domin  cikakken bincike ”

Jawabin ya bayyana .

Iyalan mamacin sun ce, Shuaibun ya bar gida ne domin zuwa cin kasuwar  Sara, wadda take ci duk ranar Talata. 
Iyalan sa sun ce sunyi matukar mamakin cewa a baki  titi aka gano gawar sa. 


Shehun yace, babban kwamandan hukumar na jiha, ya sanya jami’ai na musamman, domin su gudanar da kwakkwaran bincike a yankin. 


Ya ja hankalin mutanen yankin da kada su firgita a yayin da binciken gano musabbabin rasuwar tsohon dan shekara 55.

Jami’an tsaro ne ke bawa ‘yan ta’adda bayanan sirri – Shugaban Civil Defence

Shugaban hukumar CIvil Defence na kasa, Dr Ahmed Audi, ya ce wasu daga cikin jami’an tsaron Najeriya suna yiwa ‘yan ta’adda aiki, inda suke kai musu bayanan sirri.

Shugaban ya bayyana hakane a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gabatar kan yadda za a tsare dukiyar kasar, wanda aka gabatar a dakin taro na NAF dake babban birnin tarayya Abuja, a jiya Talata.

Ban san ko za ku yadda dani ba idan nace muku ‘yan ta’adda ba wai iya daga wajen jami’an tsaro suke samun karfin guiwa ba, wajen kai musu bayanan sirri, hatta mutanen gari suna taimaka musu, hakan ya sanya dole mu janyo sarakunan gargajiya, malaman addini, ‘yan siyasa, matasa don nemo mafita kan wannan lamari, a cewar shi.

Audi ya ce cigaba da samun matsalar tsaro, yana zama barazana ga dukiyar da abubuwan more rayuwa, inda ya bayyana jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, Borno da sauran wasu jihohin Arewa a matsayin abubuwan kwatance.

A ba mu wuka da nama mu yaki ‘yan ta’adda, bindiga bata yi mana komai – Mata mafarauta

Haka kuma yayi magana kan hukumomin tsaro da su canja tsari wajen ganin an kare dukiyar kasa daga hare-haren da ‘yan ta’addar ke kaiwa.

Audi, wanda ya nuna rashin jin dadin sa dangane da maganar Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, wanda yace gwamnatin tarayya tana kashe naira biliyan sitti (N60b) a kowacce shekara wajen gyaran bututun mai a fadin Najeriya, inda ya bukaci a canja tsari wajen kare dukiyar kasar daga bata gari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe