27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Allahu Akbar: Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a masallacin Hagia Sophia

LabaraiAllahu Akbar: Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a masallacin Hagia Sophia
Tarawih Prayer To Take Place In Hagia Sophia Mosque After 88 Years.jpg
Allahu Akbar: Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a masallacin Hagia Sophia

Labari mai dadi na isowa daga babban masallacin Hagia Sophia da ke kasarTurkiyya a birnin Istanbul, wanda ya dawo da matsayinsa na masallaci shekaru biyu kacal da suka wuce.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya labarta cewa, babban masallacin Hagia Sophia na shirin gudanar da sallar tarawihi na farko a cikin watan azumin Ramadan na bana, bayan shafe shekaru 88 ana amfani da shi a matsayin gidan tarihi.

Bayan shafe shekaru mai tsayi masallacin zai dawo da ayyukan ibada a watan Ramadan Bana

Ba wai sallar tarawihi kadai ba, an ruwaito cewa, masallacin Hagia Sophia ya kuma shirya gudanar da taruka da dama na watan Ramadan kuma ana sa ran masu ibada da yawa za su ziyarci wurin a cikin wannan wata mai alfarma.

Masallacin a baya ya kasance gidan adana kayan tarihi

Masallacin Hagia Sophia a baya ya kasance a matsayin gidan tarihi ne tun shekarar 1934. Amma, a shekarar 2020 ya dawo da babbar martaba a matsayin masallaci kuma an bude shine domin musulmi su gudanar da ibada a shekarar 2020.
Abin takaici, cutar COVID-19 ta kunno kai a Turkiyya a waccan lokacin. Hakan ya tilastawa masallatai rufewa don rage yaduwar cutar.
Cikin ikon Allah a shekarar bana, masallaci ya dawo zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a matsayin wurin ibada ga musulmi a cikin watan Ramadan; yayin da aka yi wa akasarin al’ummar kasar allurar rigakafin cutar, adadin masu kamuwa da cutar ya fara raguwa, kuma tuni an fara samun saukin kamuwa da cutar sosai.

Da duminsa: Mulhidin Kano, Mubarak Bala ya amsa laifinsa na batanci, an yanke masa shekaru 24 a gidan maza

Kotu ta yanke wa mulhidin jihar Kano, Mubarak Bala, hukuncin shekaru 24 a gidan yari bayan ya amsa laifuka 18 da ake zarginsa da su da suka hada da tada zaune tsaye da kuma hana zaman lafiya da aka zargesa da su.

Bala, wanda shi ne shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria, an kama shi a garin Kaduna a ranar 28 ga watan Afirilu a gidansa inda aka mayar da shi Kano, wurin da aka mika korafin batanci da tada zaune tsaye da yake yi da kalamansa.
Tun farko ya yi wasu wallafa da suka soki Musulunci, Allah da Annabi Muhammad a shafinsa na Facebook, lamarin da ya janyo tashin-tashina, Daily Nigerian ta ruwaito.

An dinga gangamin mika bukatar a sake shi ko kuma a gurfanar da shi inda masu rajin kare hakkin dan Adam suke cewa an hana shi ganin matarsa da lauyansa.
Amma a yayin da ya bayyana a gaban Mai shari’a Farouk Lawan na babbar kotun jihar Kano da ke lamba 4, sakateriyar Audu Bako a ranar Talata, Bala ya amsa dukkan laifukan da ake zarginsa da su.

A yayin da alkalin ya tambayesa ko ya san abinda amsa laifukansa ka iya janyo masa, Bala ya jaddada cewa ba zai sauya kalamansa na farko ba.
Lauyan Bala, James Ibor, tun farko ya yi kira ga Bala da ya sauya matsayarsa amma ya jaddada cwa ya aikata dukkan laifukan da ake zarginsa da su.

Lauyan ya bayyana fushi da tsoro a matsayin dalilan da suka sa wanda ya ke karewa ya amsa laifukan, inda yace wana ya ke karewa ya yi shekaru biyu a gidan maza.

Sai dai Bala, wanda ya bayyana ba tare da ya girgiza ba, ya daga hannunsa inda ya sanar da kotu cewa ya aikata laifukan da ake zarginsa da su.

A yayin rokon rangwame, Bala ya ce bai yi wallafarsa ta Facebook domin ya tada tarzoma ba. Ya ce ya dauka alkawarin ba zai sake maimaita irin wallafar batancin ba a nan gaba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe