32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Labari mai daɗin ji: Gwamnatin tarayya za ta gwangwaje manoma 98,000 da N5bn

LabaraiLabari mai daɗin ji: Gwamnatin tarayya za ta gwangwaje manoma 98,000 da N5bn

Gwamnatin Tarayya a ranar Laraba ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin fara shirin (GEEP 2.0) a dukkanin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

An bayyana waɗanda za su amfana da shirin

Ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin, manoma 98,000 da masu ƙananan sana’o’i za su samu bashin kuɗaɗen da ba ruwa a ciki daga N50,000 zuwa N300,000. Hakan na nufin gwamnatin tarayya za ta bayar da bashin N5bn a cikin shirin. Jaridar Punch ta rahoto.

Ministan jinƙai da walwala, Sadiya Farouq, ita ce ta bayyana hakan ta hannun mai taimaka mata Nneka Anibeze, a wata sanarwa a birnin tarayya Abuja.

Hakan ya biyo bayan kammala tantance kashin farko na waɗanda su ka cancanci amfanuwa da ƙananan basussuka daga N50,000 zuwa N300,000,”  a cewar sanarwar

Gwamnatin tarayya
Sadiya Umar Farouq, ministar jinƙai da walwala. Hoto daga jaridar Punch

Kuɗin bashi ne ba kyauta ba

Farouq ta bayyana cewa dukkanin waɗanda za su amfana da shirin gwamnatin tarayya na GEEP 2.0, za a tura musu saƙon taya murna a cikin kwanaki ma su zuwa domin sanar da su samun nasarar su da kuma ƙara tunatar da su cewa shirin bashi ne ba wai kyauta ba ne.

Ta bayyana cewa:

Nan ba da jimawa ba dukkanin waɗanda za su ci moriyar shirin za a tura musu kuɗin. Muna ƙara tunatar da su cewa bashi ne wanda za a biya ba tare da ruwa ba.

Ba kyauta ba ce ko garaɓasar gwamnati. Bashi ne mara ruwa wanda dole za a biya cikin watanni tara.

Ministirin ta bayyana cewa shirin GEEP 2.0, bashi ne wanda gwamnatin tarayya ta shirya domin samarwa mabuƙata da waɗanda talauci yayi wa katutu hanyoyin samun basussuka.

Labari mai dadi: Bankin duniya ya bawa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 311 ta rabawa talakawan Najeriya

Gwamnatin shugaba Buhari ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna NG-CARES da naira tiriliyan 311.2 domin farfaɗo da tattalin arzikin kasa

Shirin zai bayar da ƙarfi ne wajen samar da ayyukan yi da tallafa wa masu ƙananun sana’o’i da kuma ɓangaren noma

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya ƙaddamar da shirin, ya ce shirin zai gudana ne na tsawon shekaru 3 sannan za a rarraba kuɗaɗen ne a tsakanin jihohin ƙasar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe