24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Zuwa yanzu na san ‘yan Najeriya sun gane babban kuskuren da suka tafka na zaben Buhari, Tsohon janar din soji

LabaraiZuwa yanzu na san ‘yan Najeriya sun gane babban kuskuren da suka tafka na zaben Buhari, Tsohon janar din soji

Tsohon jami’in soja na daya daga cikin jihohin arewa ya ce rashin shugabanni na kwarai a dukkan matakai ne ke da alhakin hauhawar rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, musamman a yankin arewa, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce da shugabanni na gari, dakarun sojin Najeriya zasu iya gamawa da ƴan ta’adda cikin watanni shida idan suna da isassun kayan aiki.

taadda 1
Zuwa yanzu na san ‘yan Najeriya sun gane babban kuskuren da suka tafka na zaben Buhari, Tsohon janar din soji

“A yanzu, nayi imani ƴan Najeriya sun gane kuskuren da suka tafka na zaɓen Buhari, sannan sun gane cewa bazai iya riƙe kasar nan ba,” a cewarsa.

Ya siffanta hakan da abun takaici, inda ya ce a koda yaushe shugaban ƙasa a shirye ya ke da yin alawadai, sai dai yana mamaki idan yin alawadan yana tsaida kashe-kashen da ake.

Tsohon jami’in ya kara da bayyana yadda matsalar rashin tsaro ke cigaba da hauhawa, saboda masu ba Buhari shawara ba sa fada masa gaskiya.

Har ila yau, tsohon shugaban jami’an sojin kasan Najeriya ya yi alawadai da yadda mulkinsa ke kula da matsalar rashin tsaro.

Sannan ya ce, sanya bamabamai a dajika don wartakar ƴan ta’adda ba abu mai ɗorewa bane wajen kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, sannan ya yi kira ga gwamnati da ta bunciko tushen matsalar.

“Idan kana so ka kashe bishiya, dole ka ɗaɗɗako ta tun daga tushe, saboda idan ka yanke rassa ba tare da tumɓuko tushen ba, baka kashe bishiyar ba. Maganar gaskiya, zuwa dajika da sanya bamabamai abu ne mai kyau, amma a ganina, ya kamata ka tambaya, meyasa suke barin gidajensu, sannan suka zaɓi zuwa dajika don hantarar mutane? Dole mu bincika meyasa, sannan idan muka cire dalilin, zamu iya magance matsalar,” a cewarsa.

A ra’ayinsa, Kaftin Rufai Garba (mai ritaya), tsohon jami’in soja na jihar Anambra da Sokoto, ya ce yadda matsalar tsoro ke kara ƙamari a arewa yana da matukar ɗaga hankali, inda ya ƙara da cewa ya kamata ace an tattauna tsakanin jami’an tsaro da shugabannin anguwa don gano mayan abubuwa da ke haddasa hauhawar rashin tsaro a yankin.

“Ya kamata muyi aiki tuƙuru don tattara bayanan sirri da tacewa. Kowa zai ce maka ya ruɗe. Meyasa? Idan ƴan bingidan na jin haushin mulkin ne, su je su nemi masu riƙe da mulki, su cire talakawa daga ciki, bawai suje su yi ta kashe mutane a ƙauyuka ba, suna lalata gonaki da walwalar mutane, suna yiwa mata fyaɗe da halaka yara? meyasa?”, yayi tambaya.

Kaftin mai ritaya na sojin saman Najeriya, John Ojikutu ya ce tattara bayanan sirrin shi ne makulli wajen magance matsalar tsaro a kasar.

A cewarsa, idan aka rasa bayanan sirri, kokari wajen magance matsalar tsoro ba zai yi amfani ba.

Okhidievie mai ritaya ya ƙara da cewa shugaban ƙasa baya samun “Sahihan bayanan sirri” game da halin tsaron ƙasar nan, sannan ya ƙara da cewa, “Abunda ya ke samu, bayani ne wadanda aka tace.”

Haka zalika, ya kara da cewa, an siyasantar da harkar tsaro, sannan akwai buƙatar cire siyasa a cikin matsalar rashin tsaro don samun mafita mai ɗorewa.

Wani mataimakin sifeta janar mai ritaya na ƴan sanda, Ambrose Aisabor ya ce, tsarin tsaro a ƙasar nan ya rushe.

“Kuna faɗa mana, sojoji na aiki a jihohi 34 amma duk da haka babu cigaba, matsalar na nan har yanzu? ya yi tambaya.

Da dumi dumi: ‘Yan bindiga sun kashe janar din soja a hanyar Abuja

Wasu ‘da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yiwa wani babban janar ddiin soja kisan gilla akan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, bayan sun kashe shi sunyi garkuwa da matarsa, yayin da shi kuma direban shi yayi mutuwar karya.

A ranar Alhamis ne 15 ga watan Yulin shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga suka kashe Manjo Janar Hassan Ahmed, darakta a helkwatar sojojin Najeriya dake Abuja, akan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Bayan sun kashe Ahmed, wanda ba a jima da bashi mukamin darakta ba, wanda shugaban hukumar soji ta kasa Faruk Yahaya, ya nada shi, maharan kuma sunyi garkuwa da matarshi, a rahoton da jaridar Daily Nigerian ta bayar.

Direban motar yayi mutuwar karya

Wata majiya da tayi hira da jaridar Punch ta bayyana cewa a lokacin harin, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da matar Ahmed, bayan direban motar yayi mutuwar karya, inda hakan ya sanya ya tsira da rayuwar shi.

Hukumar soji ba ta bayyana cewa an sace matar sojan ba

Da take bayar da rahoto dangane da wannan lamari, mai magana da yawun hukumar soji ta kasa, Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar, bai bayyana wurin dake nuni da cewa an sace matar marigayin ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe