
Hukumomin Malaysia sun sanar da cewa za a kama duk Musulmin da aka gani yana ci ko sha a bainar jama’a batare da wani lalura ba yayin azumin watan Ramadan, za a yanke musu hukuncin tara ko dauri, ko kuma duka biyun.
Za a ci tarar duk wanda aka kama yana ci ko sha a cikin jam’a
Mataimakin babban ministan Penang I Datuk Ahmad Zakiyuddin shi ne ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda suka karya wannan doka a karkashin sashe na 15 na dokar hukunta laifuka ta Penang ta shekarar 1996.
Ya kara da cewa a cikin watan Ramadan jihar Penang da ke kasar Malaysia za ta gudanar da wani shirin hadin gwiwa, wanda hakan na daya daga cikin kokarin da mahukuntan kasar suke yi don ganin an wayar da kan al’ummar musulmi da kuma gayyatarsu domin martaba wannan wata na ramadana.
Hukumar ta ce wannan yunkuri zai kawar da duk wani aikin mara kayau a watan na ramadana
Wannan aiki na hadin gwiwa zai kawar da ayyukan da suka sabawa watan Ramadan, kamar cin abinci da sha da gangan a bainar jama’ar batare da wani laluri rashin lafiya ba.
Duk wanda ya aikata wannan laifi a karon farko, to za a ci tarar sa RM1,000 ko kuma zaman kurkukun wata shida ko kuma duka biyun.
Idan aka sake maimatawa a karo na biyu za a ci tarar RM2,000 ko ɗaurin shekara ɗaya ko duka biyun.
A cewar Ahmad Zakiyuddin, wanda shi ne shugaban kungiyar Penang Islamic Religious Council (MAINPP), doka ta 15 ba wai masu abincin kawai ta shafa ba, har ma da masu sayar da abinci, da abubuwan sha, irin su sigari, da dai sauransu.
Ya ce, Sashen Harkokin Addinin Musulunci na Penang (JHEAIPP), Majalisar Penang City (MBPP), Majalisar City na Seberang Perai (MBSP), Ma’aikatar Lafiya ta Penang, da Sashen Gudanar da Ayyukan Halal na JHEAIPP za su yi aiki tare don gudanar don hadin gwiwa wajen ganin an kawar da masu karya doka.
Akwai wurare da dama da idon hukumar zata fi maida hankali a kai
Ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu JHEAIPP ta gano wurare kusan 120 da za a sanya ido a kai sosai Bugu da kari, ayyukan za su kuma mai da hankali kan abubuwan da suka shafi tsaftar gidaje da sarrafa abinci, bin ka’idojin neman lasisi, da sauran abubuwan da suka dace a karkashin dokoki da ka’idoji dasuka dace.
Ahmad Zakiyuddin ya rufe jawabinsa inda yake fatan samun cikakiyar hadin kai tare da fata aikin zai yi nasara wajen wayar da kan al’ummar musulmi a Penang ta yadda azumin watan Ramadan na bana zai kasance mafi alheri ga kowa.
Ramadan 2022: Sunayen limamai 6 da zasu jagoranci sallar Taraweehi da Tahajjud a Masjidul Haram
Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawi da Tahajjud a masallacin Makka na azumin wannan shekarar. Wannan jerin sunayen an fitar da su ne a shafin tweeter na Haramain Sharifain, a ranar 23 ga watan Maris.
Sunayen Limamai shida 6 wadanda zasu jagoranci sallar a masallacin haramin Makka, lokacin azumin 2022, wadda za’a fara a watan Afirilu, sune kamar haka :
- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
2.Sheikh Abdur Rahman Al Sudais
3.Sheikh Saud Al Shuraim
4.Sheikh Maher Al Muaiqly
5.Sheikh Sheikh Yasir Al Dawsary
6.Sheikh Bandar Baleelah
A yadda jerin sunayen suka zo, ya nuna cewa babu wani Limami daga wajen kasar da zai shiga jerin limaman a wannan shekarar .
Haka kuma, jawabin yadda kowanne limami zai yi sallah da lokacin da zaiyi ta, shima hukumar ta fitar da jadawalin sunayen limaman dakidaki.
A baya, Musulmai na duniya sunyi murna kwarai, kasantuwar samun albishir na cewa, za’a gudanar da sallar Tarawi da Tahajjud a masallatan Makka da Madina, ba tare da fashin ko daya ba. Shugabancin hukumar kula da masallatan Makka da Madina ne ya sanar cewa, gabaki daya da yan kasa da baki duk zasu halarci sallolin a duka masallatan guda biyu.
Wannan kyakkyawan albishir ne ga daukacin musulman duniya, idan aka yi la’akari da yadda a baya a shekarar 2021, aka hana kowa yin sallolin, in banda wasu yan kalilan, wanda ya hada da mahukuntan hukumar kula da masallatan, da kuma wasu yan kadan daga al’ummar gari, saboda a wancan lokacin an sanya dokar zaman gida, kuma an hana baki shiga kasar domin dakile yaduwar cutar COVID-19.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com