An haifi wata budurwa, Nadia mai shekaru 27 da wata cuta mai suna “phocomelia syndrome”, wacce ta ke janyo nakasu a wurin halittar gabobi.

Kamar yadda shafin Beauty Studio na Facebook ya nuna, ta bayyana:
“Akwai matukar wahala rayuwa a cikin wannan yanayin musamman ga mai karancin shekaru.
“Mutane su dinga kallo na, yara suna tsoro na, idan kuma na wallafa hotunana a kafafen sada zumunta mutane su dinga sukar halitta ta.
“Takaici duk ya mamaye ni. Na kan kasa shiga cikin sa’o’i na. Ba na iya yin wasanni saboda ba a ba ni dama. Wannan ne lamarin da ya ke daga min hankali.”
Ta ci gaba da cewa yayin da ta ke girma tana fatan samun wanda zai kwantar mata da hankali kuma ya bata kwarin guiwa.
Ta ce tana jin kunyar bayyanar da kanta a gaban mutane. Sai dai daga baya na fahimci cewa babu yadda na iya. Haka nan zan amince da yadda Ubangiji ya yi ni.
Babu wani abin jin kunya a halitta ta saboda haka nan nake. Dakyar na samu na kwantar da hankalina, a cewarta.
Ta ci gaba da bayyana yadda ‘yan uwanta suka dinga kwantar mata da hankali. Yanzu haka tana iya rayuwa kamar yadda kowa ya ke yi.
Mahaifiyarta ta kasance mai ba ta kulawa da kuma kara mata kwarin guiwa, yanzu ta kwantar da hankalinta kuma tana walwala yadda take so.
Ta ce yanzu haka tana farin ciki tare da murna da irin soyayyar da ake ba ta, da abokai da kawayen da ta yi tare da kulawar da ake nuna mata.
Wata 4 tak muka yi: Budurwa ta yi nadamar daukar nauyin aurenta da saurayin ta bayan ya sake ta
Wata mata ta ta yi nadamar aurenta ta re da daukan darasussa yayin da ta kasa samun kwnciyar hankali da tsohon mijin ta kuma tsohon masoyinta. Matar mai suna June Katei Reeves ta yi soyayya da masoyin ta na tsawon shekaru 9 amma aurensu bai wuce watanni 4 kacal su ka rabu saboda rashin kwanciyar hankali da sabani
Juni ita take kula da Iyalinta
A wata doguwar hira da Lynn Ngugi a shirin Lynn Ngugi Show, ta yi matar ta ce duk da cewa ta yi aure, amma ta dauki nauyin kula da hidimar gidan yayin da shi masoyin nata baya iya kawo komai.
Matar ta kara da cewa haka ta kanace mai hidima tun soyayar su. June ta ce ta rufa wa mutumin asiri ta hanyar yin duk wata hidima data da ce a ce shi ya yi amma ita take yi inda ta siya zoben auren su kuma ta dauki nauyin shagalin aurensu.
Yadda June ta hadu da saurayin ta
Matar ta kasance ta yi rayuwa ne da mahaifiyar ta kadai ta ce ta hadu da masoyin na ta ne a harabar makarantar su a shekarar 2009 nan da nan suka shaku suka fara rayuwa tare har na tsawon shekaru 9.
Ta kara da cewa masoyin nata shi ma ya taso ne da mahaifiyar sa kawai.June ta ce a wasu lokutan soyayyar su takan fuskantan ci matsaloli kuma inda ta bada shawarar su haifi yaro ko dan farfado da soyayyarsu.Amma duk da haka zaman nasu bai dore ba suka rabu a shekarar 2018.
June ta ce su ka sake dawo tare a cikin 2020 inda suka yanke shawarar yin aure a ranar 19 ga Disamba, 2020. Amma rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya na zahiri da na badini wanda ya yi sanadiyar lalata dangantakar su ta shekaru 9.
Kadan daga cikin martanin mutane
Jiro Jiro ya ce: “Wannan ya tuna mini da wani da na sani! Mata suna yin abubuwa masu ban mamaki don neman soyayya da karbuwa.har hakan yana so ya zama kamar al’ada, “
AudreyWilliamsMusic ya ce:”Wow. Yana da matukar muhimmanci ace ‘ya’yanmu su ganmu cikin lafiyayyar soyayya domin su san yadda soyayya ta gaske take. Kuma kawai za ku iya sanin yadda ake son wani bayan ka sa yadda za ku mutunta mutum” .
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com