24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tirkashi: Bilicin na iya janyo ciwon koda, cutar daji, hawan jini da sauran cutuka ga dan Adam, Masana

LabaraiTirkashi: Bilicin na iya janyo ciwon koda, cutar daji, hawan jini da sauran cutuka ga dan Adam, Masana

Bilicin na nufin amfani da kayyayakin da zasu haskaka wurare masu duhu a fata da kuma duk ilahirin jiki don ya yi haske.

Waɗannan kayayyakin sun haɗa da amfani da mai, sabulai, da kwayoyi, ko kuma amfani sinadarai na sulɓe fata, kamar yadda shafin Healthline.com ya nuna.

bilicin
Tirkashi: Bilicin na iya janyo ciwon koda, cutar daji, hawan jini da sauran cutuka ga dan Adam, Masana

Bilicin ba ya da wani amfani

Babu wani amfanin bilicin ga lafiyar fata. Hakan baya haifar da ɗa mai ido, sannan akwai tarin matsaloli da bilicin ke haifarwa.

A lafiyance, bilicin baya da wani amfani. Amma idan ka dauki bilicin a matsayin ɗabi’arka, yana da kyau ka fahimci haɗarurrukan dake tafe dashi.

Yadda ake bilicin fata

Bilicin fata na rage yawa ko kuma samuwar sinadarin melanin a fata.

Kwayoyin halittar melanocytes ne ke da alhakin samar da sinadarin melanin.

Mutane masu duhun launin fata sun fi yawan sinadarin melanin. hasken rana da wasu kemikal na da tasiri akan samar da melalin.

Idan kayi amfani da man bilicin a fatarka, irinsu hydroquinne, su na rage yawan kwayoyin halittar melanocytes a fatarka. Wanda hakan zai yi sanadiyyar hasken fatarka.

Illolin bilicin

Ƙasashe da dama sun haramta amfani da abubuwan dake sa bilicin , saboda haɗarurrukan da ke tafe dasu.

A shekarar 2006, hukumar kula da abinci da magunguna (FDA), da sahihan majiyoyi sun fitar da sanarwa akan yadda kayayyakin bilicin ke da haɗari da tarin matsaloli.
Kayayyakin na da illa ga bil adama bisa bayyanannun hujjoji.

Wasu mayukan bilicin da aka yi su wajen Amurka na da alaƙa da illar mercury.

Amurka ta hana amfani da mercury a matsayin sinadari a mayukan bilicin, amma akwai yuwuwar ana amfani da mercury a matsayin sinadari a sauran ƙasashe.

A binciken shekarar 2014 da aka yi, gamsassun majiyoyi na mayukan bilicin na 549 sun bayyana wa yanar gizo da shagun yadda kusan kashi 12 cikin ɗari na mayukan bilicin ke dauke da mercury.

Kusan rabi daga cikin kayyayakin sun zo daga shagunan Amurka ne.

Alamomin cutar mercury sun haɗa da:

  1. Rashin ji idan an taɓa fatarka
  2. Hawan jini
  3. Kasala
  4. Cutuwa daga rana
  5. Matsalolin kwakwalwa kamar cutar daji, shafewar tunani da sauran su
  6. Cutar ƙoda.

Matan Najeriya sun kafa tarihi, sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirki yin bilicin, Bincike

Binciken da CNN ta gudanar ta janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani dangane da bilicin.

Binciken na CNN kamar yadda Gossip.com ta ruwaito ya nuna cewa matan Najeriya sun fi ko wanne mata a nahiyar Afirka siyan man sauya launin fata.

Mayukan bilicin sun fi kasuwa da kaso 75% saboda yadda matan Najeriya suke tururuwar zuwa siyan su.

Daga Najeriya sai matan Senegal ne suka fi ko wanne mata siyan mayukan da kaso 60% duk don komawa fararen fata.

Abubuwan da mata suke amfani da su wurin sauya launin fatar nasu sun hada da mayuka, sabulai, allurai da sauran su.

Bilicin yana janyo matsaloli da dama a jikin dan Adam wanda ciki akwai cutar daji (Cancer) wacce take lalata fatar jikin mutum.

Akwai alamomi da dama da ake gane mutum idan ya kasance mai bilicin, akwai bayyanar tabbai a gabobi kamar na hannu, guiwa da sauran su.

Manyan dalilan da su ke jefa mutane harkar Bilicin

Masana sun dade su na nuna illolin da ke tafe da sauya launin fatar dan Adam wanda ake kira da harkar bilicin.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, akwai dalilan da su ke sa mutane su na shiga harkar mai hadarin gaske.

Suka ko kuma kushe ga halitta musamman ga mutane masu duhun fata ya kan tunzura su harkar bisa ruwayar Daily Trust.

Shin ka taba ko kin taba kallo wani ki ka kira shi da baki fentin Allah? Bulaki? Da sauran miyagun sunaye da ake alakantawa ga bakake?

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe