24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Na tsarkake zuciyata, na yafewa duk wanda ya cutar da iyalina- Maryam Abacha

LabaraiNa tsarkake zuciyata, na yafewa duk wanda ya cutar da iyalina- Maryam Abacha


Maryam Abaca, tsohuwar matar shugaban kasar Nageriya, ta ja hankalin yan kasa da su rungumi halayyar yafiya. 


A bangaren ta, Maryam ta yi bikin murnar ranar cikarta shekara 75, tace ta yafewa duk wanda ya saba wa iyalan ta. 


Maryam din ta kara da cewa, Allah ya tsarkake mata zuciyar ta, saboda haka koyau ko gobe ma ta mutu. 


Matar marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janaral Sani Abaca, wato Maryam Abaca, a ranar Asabar 2 ga watan Afirilu, tace ta yafewa duk wanda ya sabawa iyalan ta. 


Maryam din, ta fadi hakan ne a wani jawabi da ta fitar, a wajen taron bikin cikarta shekara 75, kamar yadda jaridar The Sun suka ruwaito. 

maryam abaca
Na tsarkake zuciyata, na yafewa duk wanda ya cutar da iyalina- Maryam Abacha


Tsohuwar matar shugaban kasar Nageriyar, tace duk wani radadi zata iya yafewa saboda Allah ya tsarkake mata zuciyar ta, saboda haka daga yanzu zuwa kowanne lokaci, bata fargabar mutuwa ta dauke ta. A fadar jaridar Nigerian Tribune 


Ga kalaman Maryam din :

 “Allah ya tsarkake mini zuciya ta, kuma har yanzu ina raye. Na gode wa Allah akan hakan. Ko yau ko gobe a shirye nake na mutu, na godewa Allah ga wannan rayuwa. 


“Ga wadanda suka saba mana ko suka cutar da mu, ina amfani da wannan dama domin in ce musu mun yafe musu, ina fata zamu yafi juna, Allah ya yafe mana gabaki daya”


Haka kuma, dattijuwar mai shekaru, ta yi kira ga yan Nageriya da su rungumi halayyar yafiya ga kowa da kowa.

Jami’ar Maryam Abacha ta sanyawa daya daga cikin dakunan karatun ta sunan Marigayiya Magajiya Danbatta

Hukumar jami’ar Maryam Abacha, MAAUN, ta sanyawa dakin karatun shari’a na jami’ar sunan fitaciyyar mawakiyar Hausa, Marigayiya Halima Malam-Lasan, wacce aka fi sani da Magajiya Danbatta.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Magajiya Danbatta ta rasu tana da shekaru 85 a duniya, bayan fama da rashin lafiya a babban asibitin Danbatta a ranar Juma’a.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaba kuma wanda ya samar da jami’ar, Farfesa Adamu Gwarzo, wacce ta fito daga kasar Faransa ta samu ‘yan jarida a Kano ranar Lahadi, hukumar makarantar ta yanke shawarar karrama sunan Magajiya Danbatta, sakamakon gudummawar da ta bayar a fannin ilimi, musamman a nahiyar Arewa.

A cewar Farfesa Gwarzo, wanda yake kuma shugaga kuma wanda ya samar da makarantar Franco-British International University dake Kaduna, hukumar makarantar kuma ta karrama fitaciyyar mawakiyar da kwalin digiri.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Nigerian

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe