24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Matar aure ta sheƙe mijinta har lahira kan yunkurinsa na ƙara aure

LabaraiMatar aure ta sheƙe mijinta har lahira kan yunkurinsa na ƙara aure

A ranar Litinin 4 ga watan Afrilun 2022, wata matar aure mai ɗauke da juna biyu mai suna Omowunmi Joseph, mai shekaru 43, mai rayuwa a unguwar Odoye a yankin Alaadarin, na ƙaramar hukumar Ibadan ta arewa a jihar Oyo, ta cakawa mai gidan ta Joseph Nwanko, wuƙa har lahira da misalin ƙarfe biyu na dare yayin da yake sharar barcin sa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Tun da farko jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rigima ta barke a tsakanin ma’auratan sati biyu da su ka wuce bayan da mijin ya shaidawa matar cewa yana son yi mata kishiya daga ƙauyen sa.

Matar auren ta miƙa kan ta gaban hukuma

An samo cewa bayan ta aikata laifin, Omowunmi ta miƙa kan ta zuwa ofishin ‘yan sanda na Iyaganku inda daga nan aka wuce da ita zuwa ofishin hukumar na Yemetu, wanda ya ke kusa da inda lamarin ya auku.

Jaridar ta Daily Trust ta ziyarci ofishin ‘yan sandan na Yemetu da safiyar ranar Litinin 4 ga watan Afrilu, inda ta samu cewa an miƙa gawar mamacin zuwa mutuware.

Hukumar ‘yan sanda ba tace uffan ba

Har ya zuwa yanzu, baa ji ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Oyo, Adewale Osifefo, ba dangane da lamarin.

Kishi yasa wata matar aure ta kashe mijin ta har lahira a jihar Nasarawa

Wata matar aure mai suna Atika ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira a garin Mararraba dake ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Lamarin dai kamar yadda City & Crime suka gano, ya faru ne a daren ranar Asabar.

Ibrahim Salihu mai shekaru 37, makanike, an ce ya je dakin Atika, wacce ita ce matar auren sa farko, domin yi mata bankwana, ya tafi dakin matar sa ta biyu da suke gida ɗaya.

City & Crime sun tattaro cewa Salihu ya kasance yana kwana biyu tare da kowacce daga cikin matan a kan jujjuyawa kuma yana da dabi’ar bankwana da kowa a duk lokacin da zai tafi ɗakin ɗayar.

Kuma abin da ya yi ke nan a ranar da misalin ƙarfe 8 na dare, sai kawai Atika ta amsa a fusace ta cije shi a yatsa,” inji wata majiya daga cikin harabar gidan

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe