27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Sifetan ɗan sanda ya mutu a otal ɗin Ibadan yana tsaka da lalata da bazawara

LabaraiSifetan ɗan sanda ya mutu a otal ɗin Ibadan yana tsaka da lalata da bazawara
Fyaɗe
Borno: ‘Yan sanda sun cafke saurayin da ya yiwa tsohuwa mai shekaru 92 fyade

An tabbatar da mutuwar wani Sifeta a hukumar ‘yan sandan Najeriya mai suna Michael Ogunlade mai shekaru 47 da haihuwa a sashen Operation na Eleyele, ya rasa ransa ne yayin da yake tsaka da lalata da wata bazawarar sa a asirce, wacce aka sakaya sunan ta, an same su,ne a Otel din The Classical a.k.a White House, Oke-Ado a Ibadan.

Sun biya kudin Otel shi da bazawarar sa na ‘yan wasu mintoci ashe ajali ke kira

Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilin Vanguard cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:15 na yammacin ranar Lahadi, jim kadan bayan da su biyu suka biya kudi don hutawa na dan wani lokaci.

Wani ganau ya shaida yadda Abin ya faru

A cewar wani shaidan gani da ido, ya ce sun hadu da ni a dai dai matakala wurin sauka bene amma kasancewar ina daya daga cikin ma’aikatan Otel din ba zan iya kure ma fuskokinsu kallo ba, don haka sai na kau da kaina gefe. Bayan ‘yan mintoci kaɗan sai matar ta fito a guje tana kuka tana cewa mutumin yana cikin wani hali.

Mun yi gaggawar sanar da ‘yan sandan da ke ofishin Iyaganku, ba tare da bata lokaci ba suka iso amma kafin su kai shi asibiti mafi kusa, ya ce ga garinku.” Ta bayyana.
Wasu daga cikin rahotanni da aka samu sun ce ya mutu ne sakamakon tsawa da ta fado kansa ta gigita shi, yayin da wasu suka ce marigayin ya yi amfani da abin kara kuzari wajen saduwa da matar.

Daya daga cikin ma’aikatan otal din da ta so a sakaya sunanta ta ce: “Ban santa ba, amma yadda take bayani bayan faruwar lamarin, mun fahimci cewar mijinta ya mutu tun shekarar 2014. Har ma ta ce marigayin ne ya dauki nauyin biyan kudin hayar gidan da take zaune da kudin makarantar ‘ya’yanta sama da shekaru biyar da sauran ayyukan gida.
“Yanzu ya zanyi ta ina zan fara? Shi ne mataimakina. Ya kasance kamar mijina domin muna haduwa kowace Lahadi. Duk abinda na roka yana bani” Daya daga cikin ma’aikatan otal din ta bayyana bayan faruwar lamarin.

An kasa samun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan a waya

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Adewale Osifeso, an kasa jin ta bakinsa saboda lamar wayarsa da bata shiga.

Wata matashiya ta bayyana Yadda mahaifinta ya yi mata ciki,kuma ya dinga dirka mata kwayoyi don cikin ya zube

Wata matashiya ‘yar kimanin shekara 20 wacce aka sakaya sunan ta a ranar Alhamis ta shaida wa wata Kotu a garin Ikeja yadda mahaifinta, Akin Isaac, ya yi mata ciki tare da zubar da cikin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa, matashiyar,wanda mai gabatar da kara na jihar, Y. A. Alebiosu ya jagoranci karar a gaban kotu, ta ce tafara zama da kakar ta ne kafin daga baya ta dawo hannun mahaifinta.

Tun tana shekaru 17 ya fara lalata da ita

Matashiyar ta bayyana cewa mahaifinta ya yi mata fyade tun tana shekara 17 lokacin kullen dokar COVID-19 na shekarar 2020 a gidansu da ke Alapere, Legas.

Ta ce mahaifinta ya bukaci ta dawo hannun sa da zama a shekarar 2019 domin ta sami damar cigaba da zuwa makarantar sakandare da kuma ba shi damar kula da ita yadda ya kamata.
Matashiyar ta ce mahaifinta ya kasance yana da mata biyu abin mamaki yafara kai hannu jikinta.

“Na ji tsoro sosai,har na rokeshi ya yi hakuri ya kyaleni, amma ya je ya sayo dorina ya ajiye a kan tebur, inda ya yi amfani da ita ya yi ta jibgata saboda kawai ya yi lalata da ni
Ya yi barazanar zai kashe ni idan har na fadawa wani. Ina da shekara 17 a lokacin. Ina aji Uku karamar sakandire, na kasance mutum mai son wake wake amma lokaci daya na chanza.

“Wata rana da safe na je na sameshi na rokeshi cewar ba na son rayuwa na ya lalace amma ya yi biris da roƙona ya cigaba da aikata masha ansa. Kodaya gama na kasa fita,” inji ta.

Matashiyar ta cigaba da zayyanawa kotun cewar mahaifinta karfi da yaji ya hana ta zuwa coci.

“Na kasance ina zuwa cocin C&S amma Ya hana ni zuwa sai faston mu ya zo ya roƙe shi ya bar in cigaba da zuwa cocin.
“Mako na biyu da ya zagayo ranar lahadi,na je coci, amma sai ya sake dakatar da ni ya ce daga yanzu in dinga zuwa cocin Redeemed ni kuma na ce masa ba na son zuwa can.
Mahaifina ya yi nasarar kwace wayata, ya karya layin wayana saboda kawai kar inyi magana da ɗan’uwana ɗan kimanin shekara 27 wanda shikadai ne nake iya gayawa damuwa,ta.

“Ya taba duka na karfen tauraron dan Adam na Gotv, har sai da wasu makwabta suka bukaci in gudu inzo in zauna da su yayin da wasu ke tsoronsa saboda shi dan OPC ne,” in ji matashiyar.

Ta shaida wa kotun cewa rashin ganin al’adar ta shiya sa ta fahimci cewar tana da ciki, Inda mahaifin nata ya yi yunkurin zubar da ciki ta hanyar bata magunguna da allurai amma abin ko,gezau.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe