Wata babbar kotun tarayya a birnin Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas, ta yanke wa wasu mutum biyar hukunci bisa samun su da hannu dumu-dumu wajen satar man fetur a Najeriya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
An bayyana laifin su
Kamar yadda Lauretta Onochie, mai taimakawa shugaba Buhari ta wallafa a shafin ta na Twitter, ana tuhumar waɗanda aka yanke wa hukuncin ne da laifin dillancin man fetur ba bisa ƙa’ida ba.
A wallafar da ta mai taimakawa shugaban ƙasar ta yi, an bayyana cewa hukumar hana zamba da rashawa cikin aminci (EFCC) ita ce ta cafke waɗanda ake zargin sannan ta miƙa su a gaban kotu.
Ga abinda wallafar ta ke cewa:
Wata babbar kotun tarayya a Port Harcourt, ta yanke wa wasu mutum biyar ɓarayin man fetur, hukunci daban-daban a gidan kaso, bisa dillancin man fetur ba tare da samun lasisin da aka wajabta ba.
An bayyana sunayen ɓarayin man fetur
Sunayen waɗanda ake zargin su ne:
1. Wei Ibolo
2. Mudashiru Toaheed
3. Etim Edet
4. Martins Savior
5. Tope Alani
Manyan Kasashen duniya 10 da suka fi sauran kasashe arzikin man fetur a shekarar 2022
Idan aka ga wani batu da ya shafi arzikin man fetur na kasashe daban-daban, hankali yana karkata kan kasar Saudiyya domin an san cewa za ta kasance kan gaba, amma abin mamaki ba haka zancen ya ke ba.
Ga jerin jaddawalin kasashe 10 da ke da arzikin mai, wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta fitar. Jimillar arzikin mai a duniya an kiyasta ya kai ganga tiriliyan 1.48.
1. Venezuela kasar tana samar da mai kimanin biliyan 304,sannan a kowace rana tana fitar da mai ganga 2,489
2. Saudiyya-kasar saudiyya tana samar da mai kimanin biliyan 259,sannan a ko wacce rana tana fitar da ganga 11,545.7 na mai.
3. Iran-kasar iran tana samar da mai kimanin biliyan 209 wanda a kowacce rana tana fitar da ganga 3,538 na mai.
4. Iraqi – kasar Iraqi tana samar da mai biliyan 145 sannan a kowacce rana tana fitar da ganga 2,986.6 na mai
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com