27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

So makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa mai shekaru 85

LabaraiSo makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa mai shekaru 85

Ba tare da dubi da tazarar shekaru 60 din da ke tsakaninsu ba, wani matashi ɗan shekara 25 ya faɗa kogin son wata tsohuwa mai shekaru 85 mai suna Thereza.

Masoyan biyu, Thereza da Muyiwa sun shirya rayuwar aure duk da ƴaƴan masoyiyarsa da abokansa sun nuna rashin amincewarsu.

matashi zai yi wufff
So makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa mai shekaru 85

Muyiwa ya bayyana wa Afrimax a wata tattaunawar da suka yi yadda ya bar ƙasarsa ta Congo don karatu a jami’a inda ya kama gidan hayan Thereza tare da abokinsa.

Saurayin ya ce, a baya ya yi soyayya da ƴan mata bai jidaɗi ba, amma Thereza ta bambanta da sauran mata, sannan yana tsoron kada ta mutu da wuri.

Ga bidiyonsu a tare:

https://youtu.be/SGp29PsKfHU
So makaho ne: Matashi mai shekaru 25 ya daura dammarar yin wuff da tsohuwa mai shekaru 85

Ya ce tana kyautata masa

Kamar yadda ya shaida:

“Ina tuna ranar wata Juma’a sanda abokin zama na yayi nisan kiwo, yunwa ta kama ni, gashi bamu da abinci.

“Na galabaita kwarai. Kawai sai tsohuwar ta kawo min abinci. Yadda ta tarairaye ni ne yasa na tsunduma a kogin soyayyarta.”

“Duk da tsohuwa ce wacce tayi jika dani, amma ina matukar kaunarta.”

Yayi kira ga masu sukarsa da su sakar masa mara ya yi fitsari, saboda wacce yake ƙauna, inda yace:

“Wannan ra’ayina ne, kuma shine muradi na.”

Sun kusa shigewa daga ciki

Thereza ta bayyana tsananin ƙaunar da take wa Muyiwa kamar yadda shima yake sonta. Ta ce a shirye take da tayi wuff dashi.

A cewarta:

“Shekaru na 85. Ina da ƴaƴa 8 da jikoki 20. Idan za’ayi dubi da shekarun saurayi na, kusan sa’an jikana na biyar ne. Amma muna ƙaunar juna. A shirye nake da in zama matarsa.”

Ga wasu daga cikin tsokacin ƴan Najeriya

Abdurrahman Ahmad ya ce:

“Shegiya duniya ya ga naira yana jiran Allah ya kar giwa ƙasa, ya samu yarinya mai jini a jika yayi wuff da ita.”

Khaleepha M Salees Sumaila ya ce:

“Ba ta yi tsufa ba tunda tana da kudi, a wannan yanayin kowa ya samu wannan damar ba zai yi wasa da ita ba, duk kuma wanda ya kushe wa wannan matashin to hassada yake masa.”

So makaho ne: Yadda hamshakiyar ‘yar kasar Amurka mai digiri 4 ta yi wufff da dan achaba

Wata mata ‘yar kasar Amurka, Carey Joy ta auri wani dan kasar Kenya, Albert Wanyonyi, a Bungina a shekarar 2018.
Carey ta je kasar ne don yin wa’azi inda tace Ubangiji ne ya bayyana mata dan achaban a matsayin mijinta
don su karasa rayuwa tare.
Abinda zai ba mutum mamaki shine matsayin ta da iliminta daga fannoni daban-daban shi kuma mijinta ko firmare bai kammala ba.

Soyayyar ‘yar kasar Amurka Carey Joy da Albert Wanyonyi ita ce asalin bayani akan so makaho ne.
A lokacin da Carey ta auri Wanyonyi, ko magana da turanci bai iya ba kasancewar ya bar makaranta kafin ya kammala firamare.
A wata tattaunawa da aka yi da Wanyonyi, ya ce ya fada soyayayyar ba’Amurkiyar duk da dukansu babu wanda ya iya yaren wani.
A hirar da TV 47, ‘yar kasar Amurka mai yara biyu ta bayyana cewa digirinta hudu daga fannoni daban-daban, ciki har da fannin tattalin arziki.
Carey ta bayyana cewa Ubangiji ne ya zaba mata Wanyonyi ya zama mijinta don haka ba ta damu da rashin iliminsa ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe