Lamarin ya auku ne a yankin Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, bayan mako ɗaya da bikin, LIB ta ruwaito.
Shugaban ƴan sakan Gaida, Shekarau Ali ya ce, an kama aminin angon da mukullen gidan ma’auratan bayan angon ya kai ƙorafi.

Yayin da aka kamashi, wanda ake zargin ya bayyana yadda ya samu mukullan daga hannun ƴan uwan amaryar bayan ya musu ƙaryar zai kai wa angon.
Ali ya ƙara da cewa:
“Angon ya buƙaci da ya maido da makullen, amma ya yi burus dashi. Bayan tabbatar fitarsu daga gidan, ya buɗe gidan ya kwashe akwatinan auren da kayan abinci.”
Za a mika shi hannun ‘yan sanda da zarar an kammala bincike
Shugaban ƴan sakan ya cigaba da bayyana yadda suke bincikarsa, daga bisani zasu miƙasa ga ƴan sanda.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce sheɗan ne ya zugashi ya ci amanar abokinsa. Sannan ya nemi gafara.
Haka zalika, babban abokin angon ya bayyana yadda ya bawa angon gudunnawar sama da N400,000.
Wani ango mai shekaru 18 ya angwance da amaryarsa ‘yar shekara 16
Al’ummar yankin sun cika da mamakin wannan aure
A ranar Juma’ar da ta gaba ta ne Tilden Fulani a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi ta yi ido biyu da wani abu mai ban mamaki da al’ajabi wanda ba a saba ganin irin sa ba,inda wani dan shekara 18 mai suna Muhammad Ahmad Salihu ya amarce da amaryarsa Sumayyah Adam Ibrahim mai shekaru 16 a duniya!
Taro ya gudana cikin farin ciki da jin dadi
Majiyar Daily Reality ta bayyana cewa, taron wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na kungiyar Ahlussunnah Wal Jama’a Izala na garin Tilden Fulani an gudanar da shi cikin lumana da shagali.
Yankin Arewacin kasa Najeriya yankine da yake cike da Fulani Mabiya addinin musulunci,wannan abu ne da aka saba. Aure shine cikar soyayya da ga zarar an kai ga fahimtar juna to aure shine abu nagaba saboda gujewa aikata alfasha kafin aure.
“Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku, da salihai daga baga cikin ku. Idan sun kasance a cikin halin rashi, Allah zai wadãtar da su daga falalarSa, kuma Allah Yã kasance Mawadãci, Masani.” [Qur’an, 24:3]
Saboda haka muna taya Ango Muhammad Ahmad Salihu Murna da amaryar sa Asma’u,Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a dayyiba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com