27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Sau 3 Allah yana kira na da na amsa, yace dani Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasar Nageriya na gaba – Inji Dino Malaye 

LabaraiSau 3 Allah yana kira na da na amsa, yace dani Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasar Nageriya na gaba - Inji Dino Malaye 


Dino Malaye, tsohon sanatan yankin Kogi ta Yamma, yace Allah ne ya sanar da shi cewa Atiku Abubakar shine zai zama shugaban kasa a zabe mai zuwa .


Wannan shine karo na shida da Atikun yake neman takarar Shugabancin Najeriya, wanda a baya yayi ta faduwa. 
Kallon da mutane da yawa ke yiwa Atikun shine, cewa yana da tsantsar kwadayin mulki. 

dino malaye
Atiku Abubakar , tsohon mataimakin shugaban kasa

Allah ne ya kira ni ya gaya mini cewa Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasa

Sanata Dino Malaye, wanda ya wakilci Kogi ta Yamma yamma, a zauren majalisar dattawa ta Nageriya a zangon da ya gabata, ya bayyana cewa Allah ne ya sanar da shi cewa Atiku Abubakar shine shugaban kasa na gaba, idan aka aiwatar da zaben 2023. 


Atikun ya bayyana aniyar sa ta fitowa takarar a ranar 23 ga watan Maris  2023 a hukumance a karkashin inuwar jamiyyar sa ta PDP mai alamar laima. 


Kungiyoyi da dama gami da yan kasuwa, sun yi ta kai masa caffa ta nuna goyon bayan su ga muradun takarar tasa, inda wata kungiyar kasuwanci ta Arewa suka saya masa fam din shiga takarar na kimanin kudi Naira miliyan arba’in 40,000,000.


Tsohon shugaban kamfanin sadarwa na Daar, Raymond Dokpesi, shine ya jagoranci mekawa tsohon mataimakin shugaban kasar, fam din takarar a shalkwatar jamiyyar PDP dake Abuja. 

Jawabin Dino Malayen

Tsohon Sanatan, Dino Malaye, ya ayyana Atikun a matsayin wanda yan Najeriya ya kamata su sanya a gaba a zaben shekara ta 2023, a yayin da yake jawabi a wajen meka fam din takarar. 


Ga bayanin da yake yi: 

“Mai girma tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kware sosai wajen sanin makamar mulki da masaniyar siyasa “

“Mun zo nan ne domin gabatar da fom din nagartaccen mutum daya tilo da zai hada kan daukacin yan tarayyar Najeriya.


” Muna nan ne domin kaddamar da fam din Ronaldo da Messi na jamiyyar PDP. 

“Mutane irin mu, Allah baya kin amsa adduar mu, idan muka roke shi”

” Idan muka kira shi , baya kin amsa kiran mu. “

“Shine  (Allah) ya kira ni sannan ya ce dani Dino, nace na’am ya Ubangiji na. ya sake kirana a karo na biyu, nace na’am ya Ubangijina. Ya kira ni a karo na uku, sannan ya ce: “Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya.” 


A cikin tawagar, kungiyar da akwai tsohon sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya.

Shugabannin jam’iyyar PDP na kula makircin hana Atiku fitowa takarar shugaban kasa a 2023

FCT, Abuja – Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar ya nuna cewa jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da tsofaffin manyan sojoji sun fito sun bayyana rashin goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Atiku, mai shekaru 75, yana neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jami’iyyar PDP a zaben shekarar 2023 bayan ya tsaya takara a jam’iyyar a shekarar 2019 ya sha kasa.

Yadda wasu daga cikin jiga-jigai kuma tsofafin sojoji masu rike da madafun iko a jam’iyyar tun kafuwar ta a shekarar 1998, su ke kokarin ganin an sauya fuskar wanda zai ja ragamar tutar jam’iyyar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe