Kalaman Sheikh Khalid sun fi garkuwa da mutane muni, Sheikh Gumi

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Kalaman Sheikh Khalid sun fi garkuwa da mutane muni, Sheikh Gumi
Kalaman Sheikh Khalid sun fi garkuwa da mutane muni, Sheikh Gumi

Sanannen malamin addinin musulunci mazaunin garin ya nuna rashin jin dadinsa dangane da wa’azin da Sheikh Nuru Khalid da kalamansa akan shugaban kasa Buhari da gwamnatinsa, LIB ta ruwaito.

A hudubarsa da ya yi a ranar Juma’ar da ta gabata, Sheikh Khalid ya nuna rashin kokarin gwamnatin Buhari da kuma rashin tsaron da ya addabi kasa.

gummi
Kalaman Sheikh Khalid sun fi garkuwa da mutane muni, Sheikh Gumi

Tuni aka kori Khalid wanda shi ne babban limamin babban masalacin Apo da ke Abuja sakamakon tsokacin da ya yi wanda ya nuna rashin nadama dangane da dakatar da shi da aka yi a baya.

Ya ce kalamansa sun yi tsauri

Yayin tsokaci akan hudubar Sheikh Khalid yayin hira da manema labarai inda ya ce maganganunsa sun yi tsauri.

A cewar Gumi, limamin Abujan bai kyauta ba ta hanyar shawartar ‘yan Najeriya da kin yi zabe don kawo karshen mugayen shugabanni.

Kamar yadda ya ce kalaman Sheikh Khalid sun fi garkuwa da mutane muni.

A cewar Sheikh Gumi:

“Wadannan miyagun kalamai ne. Kiran jama’a akan su dakata daga zaben shugabanni nagari ya fi muni akan dan garkuwa da mutanen da ake yi da kuma rashin adalcin da ake yi wa gwamnati.”

Ku Bayyana Shaidar Kun Kashe Shugabannin Ƴan Bindiga, Gumi ga Sojojin Najeriya

Shahararren Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya buƙaci Sojojin Najeriya dasu gabatar da wasu shaidu da zasu tabbatar da cewa sun kashe wasu daga cikin gawurtattaun ƴan bindigar daji biyu a dajin Zamfara a makon da ya gabata.

Shehin malami Gumi ya kara jaddada cewa, babban abinda zai sa a yii nasarar kawo ƙarshen wadannan ƴan ta’adda shi ne a zauna da su a yi sasanci, kamar yadda ya sha faɗa a baya.

Mai bai wa Gumi shawara na musamman ya fitar da takarda

Mai bawa Sheikh Gumi shawara ta fannin kafafen sadarwar zamani, Tukur Mamu, ya shaida hakan ga manema labarai. Ya ƙara da cewa, yawancin abinda ke faruwa wajen farautar ƴan bindigar dajin shi ne kashe wanda bai ji ba bai gani ba.

Gumi ya ƙara da cewa:

“Mu tambayi kawu nan mu cewa, sansanonin yan bindigar da sojojin Najeriya suke iƙirarin sun ƙona na wasu daga cikin ƴan bindigar a gurare daban-daban akwai wani shaida da za ta nuna hakan.

Hakazalika, Gumi ya ƙara da cewa:


“Akwai wani Daji da muka ziyarta a jihar Niger. Mazauna wannan yanki basu da wata alaƙa ko masaniya da ƴan bindigar dajin, amma a hakan sai da suka nuna mana Rijiyoyi biyu da basu ji ba basu gani ba wannan kone dajin da sojoji sukayi har abin ya shafesu.

“Abinda ƴan bindigar suke faɗa mana shine da zarar mun ji ƙarar jirgi mu kan gudu cikin maɓoyarmu, idan ka ga sun kashe wani bai wuce ƙananan yara ba da mata ko shanu.

Gumi ya kara da cewa:

“Naji su jiya suna murna cewa sun kashe shugabannin ƴan bindigar, a misali idan kun kashe shugabansu wani ne yake maye gurbinsa na shugabanci, wani nasara aka samu kenan?


“Misali kun kashe Dogo Giɗe wanda ya fi shi tsauri ya maye gurbinsa, bayan sun kashe Buharin Daji, Bello Turji ya maye Gurbinsa, to ina nasarar da aka samu a nan? Babu wani abun murna a nan. Abin murna kawai shine idan aka ce yau sojoji sun kashe kowane ɗan bindigar daji, shine zasu yi murna wanda hakan ba abu bane mai yiwuwa.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi