29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Ubangiji ke tsiro da ganyen wiwi, ban ga laifi ba don an yi amfani da shi, Jarumin fim kuma Fasto Majid Michel

LabaraiUbangiji ke tsiro da ganyen wiwi, ban ga laifi ba don an yi amfani da shi, Jarumin fim kuma Fasto Majid Michel

Fitaccen jarumin Nollywood kuma fasto, Majid Michel ya ce Ubangiji ne ya ke tsiro da ganyen wiwi daga kasa don haka bai ga laifi ba don an yi amfani da shi ba, LIB ta ruwaito.

Yayin da yake bayani da Kent Mensah a gidan rediyo Asaase, Majid ya yi kira ga gwamnatin kasar Ghana da ta amince da saye gami da siyarwa tare da amfani da wiwi a kasar.

majid
Ubangiji ke tsiro da ganyen wiwi, ban ga laifi ba don an yi amfani da shi, Jarumin fim kuma Fasto Majid Michel

Kamar yadda yace:

“Na yi shaye-shaye a baya. Ba wai ina nufin wiwi ba. Amma ban ga laifin amfani da wiwi ba, Ubangiji ne ya ke tsiro da ita, kuma ya ke halittarta.”

Ya bayyana yadda ya yi shaye-shaye a shekarun baya, inda ya ce bai taba ganin wanda ya sha wiwi ya yi mankas ba.

Matasa su sauya salon amfani da wiwi

A cewarsa:

“Ban taba jin wanda wiwi ya yi wa yawa ba. Na sha wasu kayan shaye-shayen kamar hodar iblis da sauransu.

“Na sha abubuwan da idan yanzu na fada muku sai kun yi mamaki. Tsawon shekaru inata kokarin ganin na daina shaye-shaye.”

Majid ya ba matasa masu kasa da shekaru 25 da su kiyaye amfani da ganye. Ya shawarce su da su dinga yin shayi da ganyen maimakon amfani da hayakin shi.

Na wanke wa jarumai mata bireziyya da dan pant, inji Jarumi Mustapha Naburaska

Fitaccen jarumin barkwanci, Mustapha Naburaska ya bayyana a irin wahalhalun da ya sha a masana’antar Kannywood kafin ya kai wannan matakin da yake a yanzu a wata hira da Arewa 24 ta yi da shi a cikin shirin Gari ya waye inda ya amsa tambayoyi da dama.

A cikin hirar, Naburaska ya bayyana cewa a baya ba ya da wata daraja a masana’antar Kannywood sai dai a aike shi siyo sigari, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ya ci gaba da bayyana cewa har wankin bireziyya da dan pant ya yi wa manyan jarumai mata. Ya ce har rikon jaka ya yi musu a lokacin ba ya da wata daukaka.

A cikin bayanin da jarumin ya yi, ya bayyana yadda ake je da shi don sanya shi cikin waka, inda mashiryin shiri Rabi’u Ibrahim ya wulakanta shi.

A cewarsa, ya ce shi bai ga jarumin da za a sanya a wakar ba. Dama manyan jarumai suna bayar da labarin yadda masu shirya shiri suke raina musu wayau tare da wulakanta su.

Yanzu haka da yawan su sun zama manyan jarumai, shi kuma furodusan yana nan babu wanda ya san da shi a yanzu kuma ya ma bar harkar fim din.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe