35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Rayuwar wani direba Emmanuel Tuloe, ta Kyautata bayan ya tsinci Naira miliyan N25,000,000 kuma ya mayarwa da mai su

LabaraiRayuwar wani direba Emmanuel Tuloe, ta Kyautata bayan ya tsinci Naira miliyan N25,000,000 kuma ya mayarwa da mai su

Emmanuel Tuloe, matashi ne dan shekara 19, wanda ya bar karatutun yana matakin furamare, a sakamakon rashin gata, yanzu yana karatu a makarantar ‘yayan masu kudi, da ba ma kowanne mai gatan yake samun shigar ta ba. 


A shekarar da ta gabata, Emmanuel din yana ta gwagwarmayar yadda zai rufawa kansa asiri ta hanyar neman na kansa, sai ya tsinci wasu kudade a jakar leda a bakin titi, lokacin da yake aikin motar haya ta Tasi. 


Kudaden da ya tsinta dalolin Amurka ne kimanin $50,000 wanda yayi daidai da kudaden Najeriya, Naira miliyan ashirin da biyar N25,000,000 tare da wasu kudaden kasar Liberia. 

Emmanuel
Emmanuel Tuloe, wanda ya tsinci miliyan 25m kuma ya mayar dasu ga mai su


A wancan lokaci, Emmanuel shine mai wuka da nama akan kudin, domin zai iya yin komai dasu ba tare da kowa  ya sa masa ido ba, tunda babu wanda ya san ya tsinta, amma sai ya yanke shawarar ya kaiwa wata yar uwarsa ta ajiye kudaden. 


Bayan sun adana kudin sai yaji ana cikiyar kudin a gidan radiyo, inda baiyi watawata ba, ya dauki kudaden ya kaiwa mai su. 


Ya sha caccaka da zolaya daga abokansa, wasu har cewa suke yi zai mutu cikin talauci, amma shi bai damu ba, wanda daga baya kuma wannan kyakkyawar Halayyar ta jawo masa alkhairai masu yawa. 


Abu na farko da ya fara samu, shine yabo daga bangarori da dama, sannan wata makaranta mai suna Ricks Institute, dake kasar ta Liberia, wadda ta yayan masu hali ce, ta bashi gurbin karatu kyauta. 


Bugu da kari, shugaban kasar Liberia George Wear, ya baiwa Emmanuel din kyautar dala dubu goma, $10,000,000. Ina da shima mai gidan rediyon da ya kai kudaden, ya bashi wasu  kudade masu yawa. Shi kuma wani mai kudi ya bashi dala $1,500 duka kyauta. 


Mafi mahimmanci a duk kyautar da ya samu, shine wata jami’ar kasar Amurka da ta bashi gurbin karatu kyauta bayan ya kammala sakandaren da yake yi. 


Bayanin matashi Emmanuel akan canzawar rayuwar karatun sa


“Ina jin ` makarantar da nake, ba wai don ta yi suna ba, a’a kawai saboda kyakkyawan horo da tarbiyya da ake bayarwa a fannin koyon ilimi, ” In ji Emmanuel


Da yake Emmanuel ya bar makaranta tun yana dan shekara 9, hakan yasa bashi da kyakkyawan asasi, wato fandisho, dalilin da yasa malaman suka yi masa wani tsari na musamman. kamar yadda wani malami mai suna  Tamba Bangarori, ya shaida wa BBC. 


Zama mutumin kirki abune mai kyau 


Emmanuel ya kara da cewa:

” ya godewa Allah saboda damar da ya bashi ta aikata abin da ya dace, haka kuma ya godewa iyayen sa saboda tarayyar da suka bashi “

Wani direba da ya tsinci miliyan daya da dubu dari biyu 1.2m kuma ya mayarwa da mai shi, amma ba’a bashi ko sisi ladan tsuntuwa ba

Wani matashi dan Nageriya Emmanuel Christopher, ya sha yabo a kafar sada zumunta, sakamakon makurar gaskiyar sa da ya nuna wajen dawowa da wata fasinjar sa kudadenta da ta manta a motarsa, a Abuja. 

Daloli, fasko, da kuma sauran abubuwa masu daraja

A fadar ta, tace a lokacin da Emmanuel ya sauke fasinja mace a birnin tayya, can sai ya fahimci kamar ta manta wata jaka mai dan kumari, a kujerar baya. 

Bashi da tabbacin ta waye, kawai sai ya bude jakar, inda yaci karo da daloli, da sauran kudaden kasar waje. 

Ya iya lissafa sama da dala dubu uku $3,000 daidai da kudin Najeriya N1,247,520, da kuma wasu sauran kudaden kasashen waje. Banda ma kudin, dan tasi din ya ga katin ATM guda uku, da kuma fasko na kasashen waje guda uku. 

Ya sha zugar Shaidan akan ya gudu da kudin


Da yake yi mata jawabi akan yadda abin ya faru, da kuma yadda Shaidan ya dinga zuga shi akan ya rike kudin; sai yace: 

“Zuciya ta tayi mini magana, ni ma kuma na bata amsa


Lokacin da Emmanuel ya dawo wa da matar kudin, ta girgiza sosai, inda ta kama zubar da zafafan hawaye, amma bata bashi ko sisi a matsayin ladan tsuntuwa ba. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe