24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Da duminsa: Mulhidin Kano, Mubarak Bala ya amsa laifinsa na batanci, an yanke masa shekaru 24 a gidan maza

LabaraiDa duminsa: Mulhidin Kano, Mubarak Bala ya amsa laifinsa na batanci, an yanke masa shekaru 24 a gidan maza

Kotu ta yanke wa mulhidin jihar Kano, Mubarak Bala, hukuncin shekaru 24 a gidan yari bayan ya amsa laifuka 18 da ake zarginsa da su da suka hada da tada zaune tsaye da kuma hana zaman lafiya da aka zargesa da su.

Bala, wanda shi ne shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria, an kama shi a garin Kaduna a ranar 28 ga watan Afirilu a gidansa inda aka mayar da shi Kano, wurin da aka mika korafin batanci da tada zaune tsaye da yake yi da kalamansa.

Mubarak Bala
Da duminsa: Mulhidin Kano, Mubarak Bala ya amsa laifinsa na batanci, an yanke masa shekaru 24 a gidan maza

Tun farko ya yi wasu wallafa da suka soki Musulunci, Allah da Annabi Muhammad a shafinsa na Facebook, lamarin da ya janyo tashin-tashina, Daily Nigerian ta ruwaito.

An dinga gangamin mika bukatar a sake shi ko kuma a gurfanar da shi inda masu rajin kare hakkin dan Adam suke cewa an hana shi ganin matarsa da lauyansa.

Me ya faru a gaban babbar kotun Kano?

Amma a yayin da ya bayyana a gaban Mai shari’a Farouk Lawan na babbar kotun jihar Kano da ke lamba 4, sakateriyar Audu Bako a ranar Talata, Bala ya amsa dukkan laifukan da ake zarginsa da su.

A yayin da alkalin ya tambayesa ko ya san abinda amsa laifukansa ka iya janyo masa, Bala ya jaddada cewa ba zai sauya kalamansa na farko ba.

Lauyan Bala, James Ibor, tun farko ya yi kira ga Bala da ya sauya matsayarsa amma ya jaddada cwa ya aikata dukkan laifukan da ake zarginsa da su.

Lauyan ya bayyana fushi da tsoro a matsayin dalilan da suka sa wanda ya ke karewa ya amsa laifukan, inda yace wana ya ke karewa ya yi shekaru biyu a gidan maza.

Sai dai Bala, wanda ya bayyana ba tare da ya girgiza ba, ya daga hannunsa inda ya sanar da kotu cewa ya aikata laifukan da ake zarginsa da su.

A yayin rokon rangwame, Bala ya ce bai yi wallafarsa ta Facebook domin ya tada tarzoma ba. Ya ce ya dauka alkawarin ba zai sake maimaita irin wallafar batancin ba a nan gaba.

A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Lawan ya yanke masa hukuncin shekaru 24 a gidan yari.

An harbe ‘yan garkuwa da mutane guda 3 an kubutar da mutane a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta sanar da bindige yan garkuwa da mutane guda uku, tare da kubutar da mutane biyu da aka sace , a kauyen Katsinawa dake karamar hukumar Tudun Wada dake jihar. 
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, yace jami’an sun sami bindiga kirar AK47 ta gida, da kuma alburusai guda shida. Sannan wasu fusatattun yan sanda, sun kone wani daga cikin masu garkuwar a lokacin artabu. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe