27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Yadda na haddace Al-Qur’ani tun ina da shekaru 3 a duniya, Dan shekara 8 din da ke tafsiri a Zaria

LabaraiYadda na haddace Al-Qur'ani tun ina da shekaru 3 a duniya, Dan shekara 8 din da ke tafsiri a Zaria

Muhammad Shamsuddeen Aliyu Mai Yasin, wanda aka fi sani da Young Sheikh ko kuma Zakir MS ali, yaro ne mai shekaru 8 a duniya wanda yanzu haka yake karantar da tafsirin Al’Qur’ani mai girma.

Kamar yadda ya shaida, ya haddace Al’Qur’ani tun yana da shekaru 3 a duniya wanda daga nan ne ya daura dammarar zama babban malami.

zakir tafsir
Yadda na haddace Al-Qur’ani tun ina da shekaru 3 a duniya, Dan shekara 8 din da ke tafsiri a Zaria

Ba Qur’ani yake karantarwa ba, har da hadisi da sauran littafai duk da ya kasance yaro mai karancin shekaru amma ya tara ilimi mai tarin yawa.

A wata hira da Aminiya ta yi da shi, ya bayyana cewa ba ya wasa tare da yara masu makamancin shekarunsa saboda yadda ya kudirci zama babban malamin addinin musulunci.

Ya ce an haife shi ne a Zaria, Tudun wada, Sabon Layi a gidan Ali Mai Yasin kuma shekarunsa 8 a duniya. Ya yi karatu a Professors International Group of Schools, Zaria.

Yayin da aka tambaye shi yadda aka yi ya tara ilimi mai yawa, cewa ya yi:

“Na yi karatu ne a wurin malamaina. Wanda kuma malamai ne da mahaifina ya zabo minsu kuma sun kasance suna mayar da hankali akan karatuna sosai saboda sun ga yanayin kokarina.”

An kara da tambayarsa yana da shekaru nawa a duniya ya haddace Al’Qur’ani, inda ya bayar da amsa da:

“Kamar yadda na ji labari cewa na haddace Al’Qur’ani ne tun lokacin ina da shekaru 3.”

An tambaye shi akan me zai ce akan wadanda suke ganin kamar magani aka ba shi har ya tara wannan ilimin, inda ya kada baki ya ce soyayyar manzon Allah ce ta sa har ya kai wannan matakin. Kuma yana karanta littafin Al-Burda wanda yake saukaka masa abubuwa.

Ya bayyana lokacin da ya fara tafsirin Qur’ani da kuma irin littafan da ya kasance yana nazari akansu, har ya ce:

“Na fara tafsiri ne a shekarar 2021. Na kasance ina nazari a litattafai dayawa kafin in yi tafsiri. Amma dai daga cikinsu akwai su Jami’ul Ulumul Hikam wanda Imamu Kurtabi ya rubuta, shi ma tafsiri ne. Sannan da kuma Riyaduttafsir, na Sheikh Ibrahim Inyass. Da sauransu.”

Ya ce kuma matsawar mutum yana da mayar da hankali, komai kankantarsa zai gane karatu kuma ya iya abubuwan da ake tunanin dakyar ya iya yinsu.

‘Yan sanda sun kwaci wani matashi dakyar a hannun al’umma yayin da suke shirin kashe shi bayan ya yaga Al-Qur’ani a Kano

Wani matashi da yake sana’ar gadi wanda har yanzu ba a bayyana sunan sa ba,yana tsare a hannun ‘yan sanda bisa zargin sa da yaga Alqur’ani mai girma.

Matashin da ake zargin mai kimanin shekaru 20 a duniya, an ce jami’an hukumar Hisbah sune suka kwace shi daga hannun al’ummar unguwar Kuntau da ke cikin birnin Kano.

Daga nan kuma suka mika shi ga ‘yan sanda a halin yanzu dai mutumin yana tsare inda ake gudanar da bincike.

Iyayen gidan sa sun yi magana

Wani dan uwa mai gidan da shi matashin ya ke aiki mai suna Sunusi Ashiru ya shaida wa Daily Trust cewa mutumin ya tsira da kyar ga dukan da mutanen anguwan suka yi niyyar yi masa.

Ya ce:

Bana nan lokacin da ya aikata wannan aika aika kawai na dawo ne na ga mutane da nau’i’kan makamai a hannun su suna kokarin kashe shi.

“Lokacin da na tambaye su, sai suka labarta min abin da ya yi wanda a lokacin jami’an Hisbah suka zo suka kubutar da shi, daga bisani suka mika shi ga ‘yan sanda.”

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, Daily Trust ta tattaro labarin

Kakakin runudar ‘yan sandan jihar Kano ya yi jawabi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,shi ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya

ce mutumin da ake zargin yana hannun ‘yan sanda.

Ya yi alkawarin sanar da majiyar Daily Trust inda zai nemi cikakken bayani ga me da faruwan lamarin da kuma yadda binciken ke gudana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe