24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Bayan wata daya tal da yiwa Sayyada Sadiya Haruna daurin wata 6 a gidan yari, an sako ta

LabaraiKannywoodBayan wata daya tal da yiwa Sayyada Sadiya Haruna daurin wata 6 a gidan yari, an sako ta

Bayan wani rikici da ya barke tsakanin Jarumi kuma furodusa na Kannywood, Isah A Isah da Sayyada Sadiya Haruna a shekaru 2 da watanni da suka gabata, sun shiga kotu inda aka daureta wata 6.

Sai dai a ranar Asabar din da ta gabata ta yi wani bidiyo wanda ta tabbatar wa da duniya cewa ta fito daga gidan yari kuma zata yi azumin watan Ramadan a gida.

Bayan wata daya tal da yiwa Sayyada Sadiya Haruna daurin wata 6 a gidan yari, an sako ta
Bayan wata daya tal da yiwa Sayyada Sadiya Haruna daurin wata 6 a gidan yari, an sako ta

Ta miko godiyarta ga mutanr musamman masoyanta inda ta ce ba zata iya kiran sunaye ba don suna da yawa.

Bayanin ta a bidiyon

Kamar yadda ta ce:

“Assalamu alaikum. Ni ce Sayyada Sadiya Haruna. Masoyana na fadin duniya za ku ji ni kwana biyu shiru. Akwai wani ibtila’i ne, Allah ya jarabce ni da abinda Alhamdulillah a matsayina na ‘ya musulma na karbi wannan kaddarar hannu bibbiyu kuma wanda bai wuce kan kowa ba.

“Masoyana da suka yi min addu’a ina mika muku godiyata. Bazan iya kiran suna ba saboda in nace zan kira suna ina iya in manta da wani ban kira ba. Kar wani ya ji haushi.

“Duk masoyina wanda ya taya ni addu’a da wanda ya jajanta min akan wannan abin nan ya san kansa kuma sun san kansu ina musu godiya.

“Ubangiji Allah ya saka musu da alkhairi. Ubangiji Allah ya sa mu dauki wannan azumin a sa’a. Allah ya ba mu ikon gama shi lafiya. Ina ma kowa fatan alkhairi, ni ce ta ku Sayyada Sadiya Haruna.”

Asalin abinda ya faru

A ranar 7 ga watan Fabrairun da ta gabata ne Jarumi Isah A Isah ya bayyana cike da annashuwa inda ya shaida yadda Sayyadar ta yi masa kage wanda har ya ja suka shiga kotu kuma aka yanke mata watanni 6 a gidan yari.

A cewarsa ta yi masa sharri har ta kira shi da mazinaci kuma dan luwadi. Mutane sun taya shi murna sannan wasu masoyanta suka dinga alhini.

Daurin Sadiya Haruna nasara ce a gare ni, cewar Jarumi Isah A. Isah

Jarumin fina-finan Kannywood, Isah A. Isah wanda aka daure Sayyada Sadiya Haruna saboda shi ya fito ya nuna farin cikinsa karara dangane da hukuncin da kotu ta yanke.

Idan ba a manta ba, shekaru 2 kenan da watanni 3 bayan Sayyada Sadiya Haruna ta bayyana a wasu bidiyoyi da ta wallafa a kafafen sada zumunta tana maganganu akan Isah.

A lokacin, Sadiya Haruna ta zarge shi da yin auren mutu’a da ita, shafa mata cuta da kuma yin amfani da ita ta bayan ta ba tare da yardar ta ba.

Ta kira shi da dan luwadi, mazinaci, shege da sauran maganganu wadanda ko a lokacin ya bayyana a wani bidiyo yana musanta duk kalaman nan inda ya lashi takobin sai ya dauki matakin shari’a akan ta.

A ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairun 2022 ne labarin hukuncin da kotu ta yanke wa jarumar ya bazu jim kadan bayan jarumar ta bayyana a bidiyo tana yin wata wakar yabon ma’aiki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe