24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Yadda Muneerat Abdulsalam mai kayan mata ta sha zagi bayan ta nemi a hada mata kudi don tallafa wa talakawa da Ramadan

LabaraiYadda Muneerat Abdulsalam mai kayan mata ta sha zagi bayan ta nemi a hada mata kudi don tallafa wa talakawa da Ramadan

Fitacciyar mai sayar da magungunan mata, Muneerat Abdulsalam ta sha caccaka da zagi a kafar sada zumuntar Facebook bayan ta nemi tallafi daga mutane don ta taimaka wa talakawa.

A wata wallafar da ta yi a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ta sanya lambar asusun bankinta tana neman taimako don tallafa wa masu kananun karfi amma bata samu komai ba sai N1,500.

muneerat
Yadda Muneerat Abdulsalam mai kayan mata ta sha zagi bayan ta nemi a hada mata kudi don tallafa wa talakawa da Ramadan

Kamar yadda ta shaida a wallafa tata:

“Dazun na yi post nace a tura kudi domin a agaza wa talaka, mutum dayane kacchal ya tura naira dubu daya.

“Ba zan iya in saka sunanshi anan ba sabida ban nemi izini ba, haka ma wanda ya turo da dari biyar.

“Na gode maku sosai da yarda da kuma tayyani yin aikin lada, Allah ya amshi ibadan ku, ya kaiku gidan aljanna. Da kuma hanyar taimaka min nima in sami rahamar ubangiji.

“Toh yanzu dai ga abinda na saya da kudinda suka tura, inasa rai wasu zasu cigaba da turawa har sai ya kai yadda zamu iya bawa gajijyayu da marasa gata a wannan lokacin.

“Ga account number, 0021642480 gtb munirat Abdulsalam, ban fa ce dole sai wani ya turaba, Wanda yake da hali, komin iya kankantan, zanyi godiya.”

Sai ta wallafa hotunan abubuwan da ta siyo da kudin.

Nan da nan mutane suka hau caccakarta suna nuna cewa ba za su iya bata ko sisi ba don basu amince ba.

Ga tsokacin jama’a karkashin wallafar:

“Mummunar banza Wanda batasan darajan kanta ba.”

Wani Saifullah S Waziri ya ce:

Wannan tsokacin ya hassalata wanda ya ja har ta yi masa martani inda tace:

“Saifullahi S. Waziri tunda ka taba halittan mutum, tunda kasan menene daraja dole acikin watan Ramadan ka zagi mutum.”

Ibrahim Safiyan ya ce:

“Mu ba mu san talakawan ba sai ke kuma mu rasa wanda zamu ba wa kudi sai ke? Dallah kauce ki bamu guri.”

Ta yi masa martani cikin fushi inda ta ce:

“Ibrahim Safiyan good, ka tabbata kafin azzuminan ya kare kabi duk hanyar da za ka bi ka nemi tuba don wallahi sai na yi tsayuwar dare akan abubuwan da kuke fada, kuma Allah ya isa, ban yafe ba.”

Muzambil Adam ya ce:

“Ni kuma duk inrasa ta inda Zan taimakama mutun sai yabiyo ta hannunki?”

Ta amsa shi inda ta ce:

“Muzzambil Adam exactly, kaga Dan da ka rike? Toh wallahi sai ya yi sata inshaAllah, zai yi sata har gidan yari diga shekara sha biyar. Kayi screenshot ka ajiye, ka tuna na fadi haka.”

Shuraihabeell Muhd Ummar ya ce:

“Wanda suka baki ma zunubi zasu samu saboda da kin ci kin koshi zaki fara sabon iskanci. Kuma duk iskancin da ki ka yi suna da kamasho.”

Ta amsa shi da cewa:

“Shuraihabeell Muhd Ummar Allah ya isa, in ba ni da mumunar nufi kayi min wannan furucin toh inshaAllah sai kaga balai da iskanci a gabanka.”

Bidiyon Jarumi Adam Zango tare da Muneerat Lumansi mai koyar da kwanciyar aure ya tayar da kura

Wani bidiyo wanda ya bayyana inda aka ga Jarumi Adam A Zango, tare da Muneerat Abdulsalam wacce aka fi sani da Lumansi su na tikar rawa ya janyo cece-kuce.
Mutane da dama su na yabon jarumin tare da yabawa da halayensa tun bayan bayyanar labarin daukar nauyin karatun marayu fiye da 100 da ya yi a Zaria, cikin jihar Kaduna.

Lokacin mutane su ka dinga musanta batun yayin da wasu suke ta yaba masa.
Sannan kuma ana matukar ganin darajar jarumin bisa taimakon da yake yi wa abokan sana’arsa idan sun shiga cikin matsala, wanda hakan ya ke matukar kankaro masa girma, kima da mutunci a idon duniya duk da kasancewarsa mawaki kuma shirin fim din hausa.
Sai dai a bangaren Muneerat Abdulsalam wacce aka fi sani da Lumansi ba haka bane. Don mutane da dama ba sa ganin mutuncinta a kafafen sada zumunta saboda yadda take bayyanar da dukiyar fulaninta a waje yayin yin bidiyoyi.
Sannan ta na bayyana a YouTube da Facebook ta na koyar da kwanciyar aure babu kunya balle tsoron.
A shekarar da ta gabata ma har bayyana ta yi a wani bidiyo inda ta ce ta bar musulunci, wanda hakan ya yi matukar tayar da kura.
Bayyanar mutane biyun mabanbanta tare ya matukar razana mutane, kamar a ga dan malam da diyar boka ne.
Duk da dai ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba, amma muna fatan Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe ya kuma bamu zuri’a tsarkakakkiya, Ameen.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe