20.1 C
Abuja
Friday, December 9, 2022

 Limamin Juma’a na Abuja da aka dakatar wato Sheikh Nuru Khalid ya magantu , inda ya mai da martani

Labarai Limamin Juma'a na Abuja da aka dakatar wato Sheikh Nuru Khalid ya magantu , inda ya mai da martani

Sheikh Nuru Khalid limamin masallacin unguwar Apo dake Abuja, yayi huduba, inda yayi magana akan yadda rashin tsaro yake kara ta’azzara, da kuma matakin da ya kamata talakawa su dauka akan hakan. 


Shugabannin kwamatin masallacin na Apo, dake unguwar yan majalisa, sun kalli hudubar a matsayin ‘ ta kin jinin gwamnati’ inda nan take suka dakatar da shi. 


An dakatar da babban limamin masallacin Apo dake unguwar yan majalisa, a Abuja, Saboda hudubar da yayi a ranar juma’a 1 ga watan Afirilu. 


Shugaban kwamatin masallacin na Apo, Sanata Saidu Muhammed Dansadau, shine ya sanar da dakatar da babban limamin, wanda ya bayyana hudubar a matsayin kokarin tunzura yan  Najeriya. 

limami sheihk Nuru Khalid
Sheikh Nuru Khalid Limamin juma’a na Masallacin unguwar Apo dake Abuja


A cikin hudubar, Sheik Nuru Khalid din ya koka, akan yadda gwamnati har yanzu ta kasa kawo karshen ayyukan ta’addanci a fadin kasar Nageriya. 


Haka kuma, ya shawarci al’umma akan matakin da ya kamata su dauka, idan har gwamnati ta kasa samar musu da tsaro. 


Shehin malamin yace: 


“Matsaya daya kawai ya kamata talakawan Najeriya su dauka, wadda itace – ‘ku kare mana rayukan mu; sai mu fito zabe’ ku bari a kashe mu ; bazamu fito zabe ba, tunda dai su zabe shi suka sani”


Kwamatin masallacin sun bayyana dalilin da yasa suka dakatar da limamin 


Shugaban kwamatin masallacin na Apo, Sanata Saidu Muhammed Dansadau, yace

an dakatar da rigimammen limamin ne Saboda wata huduba da yayi, wadda ka iya tunzura al’umma “. 


Dakatar da limamin kamar yadda aka watsa a kafar BBC ta sai baba ta gani ce.


A cikin sakon da aka fitar a dai ita kafar BBC din, shugaban kwamatin masallacin ya bayyana sakon dakatarwar kamar haka : 

 “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.”

“An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ‘yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.”


 “ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da waɗanda suka saɓa wa Allah, da masu zaɓe da kuma ƙasa.”


Limamin da aka dakatar ya bara


Da yake mai da martani, Khalid din, wanda ake kira ( digital Imam) yace,” “Allah shi ne mai iko, kuma shi kadai ke baiwa mutum mulki kuma ya sauke shi, a duk sanda ya so”


Sannan limamin ya kara shawartar yan Najeriya da su dage da add’ua ga kawunansu, kasa da kuma shugabanni.

Bidiyon hudubar da Sheikh Nuru Khalid Khalid ya yi wacce ta sa aka tube shi daga limanci

Fitaccen malami kuma limami, Sheikh Nuru Khalid ya yi wata huduba a ranar Juma’ar da ta gabata wanda ya janyo har aka tube shi daga limanci.

LabarunHausa.com ta nemo wa’azin a Tashar Tsakar Gida ta Youtube inda ta rubuta muku don kowa ya san kalaman da ya furta a cikin bidiyon.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe