24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Harin jirgin kasa : Sai mun tseratar da duk fasinjojin da aka sace: Inji Hukumar Jirgin Kasa ta (NRC)

LabaraiHarin jirgin kasa : Sai mun tseratar da duk fasinjojin da aka sace: Inji Hukumar Jirgin Kasa ta (NRC)

Hukumar Kamfanin  jiragin kasa ta Najeriya (NRC), ta sake nanata kokarin da take yi na hada kai da jami’an tsaro, domin kubutar da ragowar fasinjojin da ba’a gansu ba, yayin da aka kai hari kan jirgin kasa mai lamba AK9, wanda yake jigila daga Abuja zuwa Kaduna. 

Karin mutum biyu da aka sace a harin jirgin sun dawo


Manajan daraktan hukumar Mr Fidet Okhiria, yace, an sake gano wasu mutum biyu wadanda suka kubuta, wanda ya zamana mutum 172 ne yanzu wadanda suka tsira. 


JIrgin kasa Naija 2
Sai mun tseratar da duk fasinjojin da aka sace: Inji Hukumar Jirgin Kasa ta (NRC)

“Kamfanin ya tabbatar kubutar jimillar mutane 172, wadanda harin ya ritsa dasu, inda mutane 21 kuma har yanzu ba’a gansu ba.”


“Muna sanar da fasinjojin mu masu kima, cewa kamfanin mu, hadin gwiwa da jami’an tsaro, yana iya matukar kokari wajen ganin mun tseratar da fasinjojin mu wadanda aka rasa a duk inda suke “

“Haka kuma,  kamfanin dai yana kara, jajantawa iyalan wadanda abin ya ritsa da su, da kuma, meka sakon gaisuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayuwar su”


” Sannan kuma, muna kara nuna tausayawar mu ga wadanda suka jikkata munanan raunuka, da duk ma wadanda suke cikin jirgin mai lamba AK9 a ranar Litinin 28, saboda mummunan yanayin da kuka shiga ciki. “Ya fada

Harin Jirgin kasa Daga Abuja zuwa Kaduna:Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka-Amaechi

Ministan sufuri Amaechi wanda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci wurin da harin ya faru, ya ce za a iya kaucewa faruwar wannan lamarin da ace an samu na’urar tsaro ta dijital ta kimanin Naira biliyan 3.
Ya ce yanzu sai an kashe sama da Naira biliyan 3 don gyare gyaren abubuwan da aka yi hasara yayin da aka harin hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Mun san daga ina matsalar ta ke. Muna da buƙatar samun kayan tsaro na dijital.

Karamin aiki ya ja babba hasara

“Saboda da ace muna da waɗannan kayan aikin, ba za ku ga kowa a kan wannan hanyar ba. Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka. Yanzu, gashi abinda ya faru, Mutane takwas sun rasa ransu, mutane 25 sun jikkata suna kwance a asibiti,Mutanen da aka sace bamu san adadin su ba , kudin kayan aikin da za a sa wannan digital din Naira biliyan uku ne kacal. Gashi yanzu anyi asarar abin da ya haura Naira biliyan uku.gashi an la’anta hanyoyin jirgin mun rasa abin hawa da masu horar da matuka jirgin. Mun yi hasarar mutane, Kuma kayan aikin bai fi karfin mu ba Naira biliyan uku ne kawai.

“a yanzu sai an kashe sama da Biliyan uku domin gyaran abubuwan da aka rasa a yanzu, zai kashe mu fiye da Naira biliyan 3. Kuma a halin da ake ciki a yanzu ko an bamu izinin saya zai bada wahala a da dala N400, yanzu ta koma N500. In kace zakayi gaskiya a gwamnati mutanen da kake tare da su suna kawo maka cikas,dole kaji bakin ciki.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe