24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

An harbe ‘yan garkuwa da mutane guda 3 an kubutar da mutane a Kano

LabaraiAn harbe 'yan garkuwa da mutane guda 3 an kubutar da mutane a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta sanar da bindige yan garkuwa da mutane guda uku, tare da kubutar da mutane biyu da aka sace , a kauyen Katsinawa dake karamar hukumar Tudun Wada dake jihar. 


Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, yace jami’an sun sami bindiga kirar AK47 ta gida, da kuma alburusai guda shida. Sannan wasu fusatattun yan sanda, sun kone wani daga cikin masu garkuwar a lokacin artabu. 

garkuwa
Yaran da akayi garkuwa da su a garin Katsinawa karamar hukumar Tudun Wada, a jihar Kano

Yadda labarin yan garkuwar ya ishe ‘yan sandan


Da yake kara bayani, Kiyawan yace, sun sami  labarin ne da misalin karfe 0130hrs, alissafin jami’an tsaro, wato karfe, 1:30 na dare kenan, cewa yan bindiga sun yiwa gidan wani Elisha Aminu dake kauyen Katsinawa a karamar hukumar Tudun Wada, inda suka sace yayan sa mata guda biyu,  Zainab Elisha, yar shekara 18, da kuma Nafisa Elisha, yar shekara 16, sannan sun gudu dajin Falgore. 


Karbar sakon ke da wuya, nan da nan, sai kwamashina CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bazaka, inda ya umarci, rundunar sunturi ta (  Puff Adder) karkashin jagorancin SP Kabir Aminu, wanda shine DPO na Tudun Wada, da kuma jami’ai daga sashen yaki da garkuwa da mutane, karkashin jagorancin SP Shehu Dahiru, domin su kubutar da yaran kuma su kamo masu laifin. 


” Nan da nan rundunonin suka fara aikin su a tare, da taimakon wasu, yan agaji da ake kira   ‘Yan Bula’ “. 


” Tuni aka zagaye dajin, inda aka yi wa barayin talala. Anyi musayar wuta na tsawon awoyi biyu,”


” An sami nasarar harbe yan garkuwar, inda aka tseratar da yaran ba tare da rauni ba. Suma jami’an babu wanda ya ji rauni ko daya “


 “An samu wata bindiga AK47 kirar gida, sannan kuma wani fusataccen dansanda ya kone daya daga cikin yan garkuwar “. 


Kiyawa din ya kara da cewa, an kai gawarwakin yan ta’addan, babban asibitin karamar hukumar Tudun Wadan inda likita ya tabbatar da mutuwarsu, su kuma yaran tuni aka sada su da iyalan su. 


A fadar sa, yace Kwamashinan yan sanda, yana gargadin duk yan ta’adda cewa basu da maboya a jihar Kano, saboda haka kodai su tuba, ko kuma su bar jihar, idan kuma ba haka  ba, to za’a kamosu, kuma su fuskanci fishin shari’a.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukuma tare da wasu mutum 5

Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane biyar a wurare daban-daban a jihar Ekiti a ranar Litinin 31 ga watan Janairun shekarar 2022.

Wata majiya ta bayyana cewa a harin da ‘yan bindigar suka kai na farko, sunyi awon gaba da tsohon shugaban karamar hukumar Ilejemeje dake jihar Ekiti, Bamgboye Adegoroye, da kuma wani da suke tare dashi a cikin motar shi, inda a hari na biyu kuma sun sace mutane uku da suke aiki a wata masana’antar sarrafa gawayi.

An sace tsohon shugaban karamar hukumar a motarshi tare da abokin shi

A rahoton da jaridar Punch ta ruwaito, shugaban karamar hukumar Ifesowapo, Mr Kayode Akerele, shine ya fara magana akan faruwar lamarin, inda ya ce Adegoroye da wani mutum anyi garkuwa da su a lokacin da suke cikin mota akan hanyar Isan-Iludun ranar Litinin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe