29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Bidiyon hudubar da Sheikh Nuru Khalid Khalid ya yi wacce ta sa aka tube shi daga limanci

LabaraiBidiyon hudubar da Sheikh Nuru Khalid Khalid ya yi wacce ta sa aka tube shi daga limanci

Fitaccen malami kuma limami, Sheikh Nuru Khalid ya yi wata huduba a ranar Juma’ar da ta gabata wanda ya janyo har aka tube shi daga limanci.

LabarunHausa.com ta nemo wa’azin a Tashar Tsakar Gida ta Youtube inda ta rubuta muku don kowa ya san kalaman da ya furta a cikin bidiyon.

sheikh nuru
Bidiyon hudubar da Sheikh Nuru Khalid Khalid ya yi wacce ta sa aka tube shi daga limanci

Malamin ya kada baki ya ce:

“Maganar gaskiya harkar tsaro a Najeriya ta zama kasuwanci. Wasu suna diban kudin kasa da sunan tsaro. Wannan shi ne gaskiyar abinda ya ke faruwa a kasar nan.

“Harkar tsaro ta zama kasuwanci. Ni kuma zan kara muku da cewa, jinin talaka ya zama kayan kamfen a kasar nan. Don me lokacin da zabe ya zo sai kashe-kashe ya karu?

“To kamata ya yi talakan Najeriya ya gaya wa ‘yan siyasa ko dai ku hana kashe mu ko kuma mu ki yin zabe. Sharadin mu kenan.

“Idan ba ku sa an dena kashe mutane da ranar zabe ba to mu ba za mu fito ranar zabe ba. Domin ran mu ya fi wata demokradiyya. Duk duniya demokradiyya kare ran dan Adam ya kamata ta dinga yi ba kashe mutane ba a banza a wofi ba.

“Wai ace hanyar jirgin kasa a sanya mata bam, kuma a biyo da harbe-harbe. Kuma wai a shiga cikin first class ace kai ne wane zo nan! Wato ‘yan ta’addan sun fi jami’an tsaron Najeriya samun intelligent reports.”

Ana zargin a cikin manyan kasar nan akwai masu basu kayan aiki da labari kamar yadda malamin ya shaida.

Ya ci gaba da cewa ya kamata a sanya wa hukuma sharadi akan cewa ko dai a dena kashe mutane ko kuma a dena yin zabe gaba daya.

Ya ci gaba da korafi inda ya ce talaka yana ta hakuri talauci, tsadar rayuwa, karya da sauransu amma duk da haka ana yunkurin hana mutane rayuwa ta hanyar rashin tsaro.

Wannan jawabin nashi ya janyo cece-kuce wanda yasa nan da nan gwamnati ta dakatar da limancinsa da tunanin zai dinga yada abubuwan da zasu tayar da hankula.

Da fatan Allah yasa mu dace amin.

Sheikh Nuru Khalid – Mun jima muna yiwa Shugaba Buhari addu’a amma har yanzu babu abinda ya canja

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Apo Legislative dake Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya bayyana cewa iya addu’a kawai ba za ta kawo karshen matsalar tsaron Najeriya ba.

A cewar fitaccen Malamin da mutane da dama ke girmamawa, ya ce har yanzu babu wani abu da aka samu canji akai, domin kuwa Malaman addini sun jima suna yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a.

Ya bayyana hakane a wata hira da yayi da jaridar Punch.

Maganar gaskiya shine ba zai yiwu mu ce komai addu’a ce za ta yi mana maganin shi ba. Shin ma ayi masa addu’a yayi me? Ni kawai zan iya yi masa addu’a ne ya tashi yayi abinda ya dace ba wai ya zauna yana kallon abubuwa na faruwa ba tare da yayi komai ba.

Addu’a ba ta yin aiki a haka, shi yasa nace idan yana son cika alkawuran da ya dauka, Allah ya taimaka mishi. Bayan haka kuma, mun jima muna yi masa addu’a amma har yanzu babu wani sakamako da aka samu.

Yayin da kuma ‘yan Najeriya ke cigaba da sanya albarka ga Malamin akan fitowa da yake yi yana fadar gaskiya ba tare da tsoro ko shakka ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe