Gwamnatin tarayya da ta jiha sun dade da sakin ragamar shugabanci, Jega

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Gwamnatin tarayya da ta jiha sun dade da sakin ragamar shugabanci, Jega
Gwamnatin tarayya da ta jiha sun dade da sakin ragamar shugabanci, Jega

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce gwamnati a dukkan matakai ta yi watsi da ragamar shugabanci, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabi a gangamin jam’iyyar PRP da ya gabata a Abuja, ranar Asabar, 2 ga watan Afirilu, tsohon shugaban hukumar INEC din ya ce babu ƙasar da zata cigaba ba tare da shugabanci mai kyau ba.

jega2
Gwamnatin tarayya da ta jiha sun dade da sakin ragamar shugabanci, Jega

A cewar Jega:

“Gwanatin mu a matakin jiha, ƙaramar hukuma da matakin tarayya sun daɗe da yin watsi da shugabanci.

“Kama babu ƙasar da za ta cigaba ba tare da shugabanci na kwarai ba, da kuma mutanen ƙwarai sun ki yin jagoranci na ƙwarai.

“Saboda haka, ina janyo hankalinmu da mu koma mu fahimci cewa akwai babban aiki a gaban mu; za mu iya ganinshi da wahala, amma bai fi karfin mu ba.”

APC da PDP sun yiwa Jega taron dangi, saboda yace ‘Yan Najeriya su yi watsi da su a 2023

A ranar Litinin ne 2 ga watan Agusta, babbar jam’iyya mai mulki ta APC da jam’iyyar adawa ta PDP suka yiwa tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Attahiru Jega, saboda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da su a zaben 2023.

Jam’iyyar ta APC da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, duka sun yi Allah wadai da wannan magana ta Jega a cikin sanarwa da suka fitar a Abuja.

A cikin hirar, Jega ya bukaci ‘yan Najeriya kada su yarda da duka jam’iyyun guda biyu idan aka zo zaben 2023, saboda duka sun ci amanar kasa a lokacin da aka basu dama.

Ya ce duka jam’iyyun guda biyu an basu dama kuma duk sun kasa yiwa kasa komai sama da shekaru 20 da suka yi suna mulki.

Jega ya bayyana duka jam’iyyun guda biyu a matsayin Danjuma da Dan Jummai idan har ana maganar cin hanci, ya kara da cewa Najeriya za ta isa tudun na tsira idan ta samu jam’iyya da za ta iya fito da ita daga cikin kuncin da take ciki.

Tsohon shugaban INEC din ya ce:

Abubuwa marasa kyau da wadannan jam’iyyu suka yi a ‘yan shekarun nan, ‘yan Najeriya kada su kara aminta da su. Yanzu ta tabbata cewa wadannan jam’iyyu baza su taba canjawa ba, koda kuwa an basu wata damar.

Ya bayyana cewa jam’iyyun guda biyu duka abu daya suke yi, saboda idan aka samu dan siyasa da laifin cin hanci a PDP, sai ya canja jam’iyya cikin sauki ya koma APC ya cigaba da wannan hali nashi ba tare da wata doka ta hau kanshi ba.

Jega ya ce:

Jam’iyyar APC da PDP sune suke da gwamnati; duka mu shaida ne. Ba su zo da wata niyya mai kyau ba ta kawo gyara. Idan kuka yi duba akan yaki da cin hanci, duka wadannan mutanen da ya kamata ace an yanke musu hukunci, suna koma jam’iyyar APC ne.

Babu abinda muke ji daga bakin gwamnati game da su. Wannan dalilin ne ya sanya na koma jam’iyyar PRP. Ni dan jam’iyyar PRP ne kuma ina neman hanya da zan taimakawa Najeriya.

Tun shekarar 1979, ina koyarwa a jami’a, kusan shekaru 40 yanzu. Daga abinda na karanta kuma na gano, a lokacin da nake shugaban INEC, zancen gaskiya, yadda naga ‘yan siyasar mu na yin zabe da kuma yadda suke mulkar al’ummar su idan sun ci zabe abin na bani tsoro.

A nata bangaren, jam’iyyar APC ta bayyana cewa zancen Jega bashi da makama, a wata sanarwa da ta figtar ta bakin Sakataren jam’iyyar, Sanata John Akpanudoedehe.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: PUNCH

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi