Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa
Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa

An yi ram da wani barawon kaji wanda ya rasa inda zai boye su sai cikin wandonsa, LIB ta ruwaito.

Wani mutum dan kasar Ghana ya yi yunkurin boye kajin da ya sace a cikin wandonsa, daga bisani ya sanya wandon don kada a gane shi.

Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa
Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa

Sai dai buyar bata yuwu ba bayan mutane sun farga inda suka kama shi da kajin dumu-dumu.

Mazauna yankin sun kama shi sannan suka cire kajin daga wandon nasa yayin da suka dinga yi masa bidiyo.

Ga bidiyon a kasa:

Shaidan ne ya umarce ni da satar wayoyi a motar ‘yan sanda, Barawo a gaban kotu

Wani mutum mai shekaru 47, da aka gurfanar gaban kotun Milimani a Nairobi, ya yi ikirarin cewa shaidan ne ya tura shi sata daga motar ‘yan sanda, LIB ta ruwaito.

Muhammad Noor ya bayyana wa kotu yadda aka umarce shi da satar wayoyi biyu, mallakin OCS a Samburu.

Noor ya amsa laifin sa na satar wayoyin wani jami’in dan sanda, Adan Shukri.

Kamar yadda ya shaida:

“Shaidan ne ya umarce ni da in saci wayoyi daga motar ‘yan sandan. Shaidan na da karfin iko.”

OCS, wanda ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Suguta a yankin Mar Mar Samburu, ya je Nairobi don aiwatar da wani aiki.

An zargi Noor da satar wayoyin daga motar ‘yan sandan kirar Land cruiser a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2022, a wurin ajiye motoci na Taumeed, kusa da titin river dake Nairobi.

A wannan ranar, ‘yan sanda daga babban ofishin su sun fita sintiri, inda suka yi arangama da barawon da mutanen unguwa suka kama.

Sun sake kama wanda ake zargin, wani Muhammad Noor, wanda ke rike da wayoyi guda biyu, daga bisani suka kai shi ofishin ‘yan sandan.

An samu bayanai daga wayoyin, yayin da jami’an binciken suka tuntubi mai su.

“An tuntube shi, sannan aka tabbatar masa da cewa, an sace masa wayar amfanin shi da ta wajen aikin sa a motar ‘yan sanda, kirar Land cruiser a wurin Tahmeed, a lokacin da yake neman tiketi zuwa Kwale don aiwatar da wani aiki, wanda ya riga ya shaida wa babban ofishin ‘yan sanda.”

Noor ya amsa laifin shi gaban babbar kotun Nairobi ta Bernarda Ochoi, gami da rokon sassauci, inda ya ce shaidan ne ya umarce shi da yayi satar.

“Mzee ya nemi ayi mishi afuwa, Shaidan ne yayi min jagora zuwa motar yan sanda kirar Land cruiser, sannan ya ba ni umarnin satar wayoyin,” inji shi.

Yayin da kotun majistaren ta tambaye shi inda ya hadu da shaidan din, ya tabbatar da cewa, sun hadu wurin Nairobi a lokacin da yakai ziyara.

Haka zalika, ya bayyana wa kotu yadda aka kwantar da matar sa a asibiti a lokacin da zata haifar musu yaron su, sannan ya roki kotu da ta ba shi dama ta karshe, inda yayi alkawarin bazai sake maimaita laifin ba.

Alkali mai shari’a, James Gachoka ya umarci kotun da ta bada wayoyin ga OCS, tunda duk mallakin hukumar ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi