Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun ta bayyana cewa ta cafke wani matashi mai suna Ibrahim Sikiru, mai shekaru 27, bisa zargin halaka mahaifin sa da adda a yankin Onipanu a cikin jihar. Jaridar Pulse.ng ta rahoto
Hukumar ‘yan sanda ta yi ƙarin haske kan lamarin
Kakakin hukumar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ga manema labarai a Ota, inda ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne a ranar 30 ga watan Maris.
Oyeyemi yayi bayanin cewa an cafke matashin da ake zargin ne bayan wani mai suna Abiodun Sunday, ya shigar da ƙorafi a ofishin hukumar ‘yan sanda na Onipanu.
Sunday ya cigaba da bayani cewa wani maƙwabcin mamacin, wani mai gadin dare, Mumuni Ibrahim, wanda ya kawo rahoton cewa mamacin ya tambayi ɗan na sa dalilin da yasa ya ke barci bayan ya dawo ya same shi a gida daga wurin aiki.
Matashin ya fusata saboda an tayar da shi daga barci
Bayan samun rahoton, DPO ɗin Onipanu, CSP Bamidele Job, ya tura jami’an sa zuwa wurin da lamarin ya auku inda aka cafke wanda ake zargin sannan aka miƙa mahaifin zuwa babban asibiti domin duba lafiyar sa.
Ya ƙara da cewa, lokacin da mahaifin ya tambayi ɗan nasa dalilin yin barci a wannan lokaci, yaron ya fusata inda ya ɗauko adda ya sassari mahaifin na sa a wurare biyar.
Bayan samun rahoton, DPO ɗin Onipanu, CSP Bamidele Job, ya tura jami’an sa zuwa wurin da lamarin ya auku inda aka cafke wanda ake zargin sannan aka miƙa mahaifin zuwa babban asibiti domin duba lafiyar sa.
Wanda ake zargin, wanda ake kyautata zaton cewa ɗan daba ne, bai bayar da wani gamsashshen dalilin aikata wannan laifin ba a yayin gudanar da bincike.
A ranar 31 ga watan Maris, mahaifin ya rasu yayin da yake amsar magani a asibitin, inda ‘yan’uwansa su ka haƙiƙance kan binne sa kamar yadda addinin sa ya tanada. A cewar sa
A cewar sa
Matashi ya rotse kan mahaifinshi da tabarya ya mutu har lahira a jihar Yobe
A jiya Laraba 9 ga watan Fabrairu 2022, Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ta ruwaito cewa wani matashi dan shekara 20, mai suna Mai Goni, ya kashe mahaifinshi, Goni Kawu da tabarya a Masaba, cikin karamar hukumar Bursari.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, shine ya sanarwa da Kamfanin Dillancin Laabarai na Najeriya (NAN), cewar lamarin ya faru ranar Talata da misalin karfe 7:30pm na dare.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com