29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Abin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar mutuwar mahaifiyata, Jaruma Momi Gombe

LabaraiKannywoodAbin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar mutuwar mahaifiyata, Jaruma Momi Gombe

Jarumar Kannywood, Maimuna Abubakar wacce aka fi sani da Momi Gombe ta ce ranar da ta fi ko wacce rana farinciki a rayuwarta da kuma bakinciki ita ce ranar da mahaifiyarta ta kwanta dama.

Ta bayyana hakan ne a shirin BBC Hausa mai suna Daga Bakin Mai Ita. A ranar 31 ga watan Maris din 2022 ne BBC Hausa ta wallafa bidiyon tattaunar da ta yi da jarumar.

momi gombe
Abin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar mutuwar mahaifiyata, Jaruma Momi Gombe

Da farko ta fara da gabatar da kanta inda ta ce ta yi firamare da sakandare a garin Gombe. Sannan duk rayuwarta a cikin garin ta yi, sai yanzu kuma sana’a ta mayar da ita garin Kano.

Ta bayyana yadda ta fara fim

Ta shaida yadda ta shiga fim ta hannun wani mai gidanta Usman Mu’azu, kuma dan garinsu ne sannan ya saba da ‘yan uwanta.

Ta ce idan ‘yan fim suna aiki yana burgeta hakan yasa idan aka aiketa kai musu abinci take tsayawa ta dinga kallonsu. Daga nan ya sanyata a shirin.

Ta ce ya tuntubi mahaifiyarta daga nan ta amince inda aka sanyata ta fara shirin fim. Ta ce tana matukar farinciki da alfahari da wakar Jarumar mata wacce suka yi bidiyon da Hamisu Breaker.

Ta ce babu wata soyayya da ke tsakaninta da Mawaki Breaker, kawai mutane ne suka fadin hakan.

Sunusi Oscar 442 ne mai gidanta nan a Kannywood kuma babanta, sannan shi ne darektan da ta fi so.

Ranar mutuwar mahaifiyarta ce ranar farin ciki da bakin cikinta

Yayin da aka tambayeta abinda ya ke sata farinciki sai ta kada baki ta ce:

“Abinda ya ke sa ni farinciki shi ne ibadata. Duk lokacin da na ji ina ibada, ina samun farinciki.”

Abinda ya ke sa ta bakin ciki shi ne idan ta tuna mutuwar mahaifiyarta.”

Ta kara da cewa:

“Abin farincikin da ba zan iya mantawa da shi ba shi ne ranar da mamata ta rasu. Rabuwata da ita ta karshe shi ne ranar bakincikina kuma ranar farincikina.”

An tambayeta dalilin da yasa ta yi farinciki a ranar da mahaifiyarta ta mutu shi ne ta ce:

“Abinda yasa na ke farinciki shi ne ni ce wacce na yi maganar karshe da ita kaf a cikin ‘yan uwana. Kuma ni kadai nasan irin maganganun da muka yi da ita da irin addu’o’in da ta yi min.”

An ɗaura auren jaruma Nafisa Ishak wacce ta zagi Sheikh Aminu Daurawa

Jarumar Kannywood Nafisa Ishak ta angwance ita da mijinta.

An walliyon auren Nafisa Ishak

A wani faifan bidiyo da tashar Duniyar Kannywood ta wallafa na bikin jaruma Nafisa Ishak, an nuna mijin da ta aura suna nunawa junan su shaukin ƙauna.

Haka kuma a cikin bidiyon an nuna wani wuri inda anan ne aka ɗaura auran jarumar da mijin na ta.

Ita kanta jaruma Nafisa Ishak ta wallafa bidiyon ta angon na ta a shafin ta na Tiktok da Instagram tana faɗin “Alhamdulillah.

Ta goge duk wata wallafar da tayi a baya

Sannan kuma jarumar ta goge duk wata wallafa da tayi a baya inda ta bar kawai na ɗaurin auren da kuma wanda ake kai ta ɗakin miji.

A kwanakin baya dai Nafisa ta tsinci kanta cikin wata taƙaddama bayan tayi raddi ga shahararren malamin addinin nan Sheikh Aminu Daurawa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe