24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Tun kafuwar Najeriya ba a taɓa samun ingantaccen shugaba irin shugaba Buhari ba -Gwamna Masari

LabaraiTun kafuwar Najeriya ba a taɓa samun ingantaccen shugaba irin shugaba Buhari ba -Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa tun lokacin da aka haɗe Najeriya a 1914, ƙasar bata taɓa samun ingantacciyar gwamnati da shugaban ƙasa irin shugaba Buhari ba. Jaridar The Guardian ta rahoto

Gwamnan ya faɗi haka ne ranar Asabar a Katsina yayin wani gangami wanda masu amfana da shirin gwamnatin tarayya na ‘Social Investment Programme’ (NSIP), na jihar su ka shirya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rahoto cewa, an shirya gangamin ne a ƙarƙashin jagorancin shugabannin ‘Social Protection and Good Family Value Initiative’ (SPGFVI).

An bayyana maƙasudin taron

Maƙasuɗin gangamin shine domin yin kira ga gwamnatin tarayya da majalisar dokoki ta ƙasa da su ƙirƙiro dokar da za ta mayar da shirin na din-din-din.

Shugaba Buhari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a wurin taron. Hoto daga jaridar The Guardian

Shugaba Buhari ya ciri tuta

A cewar Masari, shugaba Buhari ya kafa muhimmin tubali wanda idan gwamnatin da ta gaje shi ta ɗora akai, zai taimaka wajen cire ‘yan Najeriya daga raɗaɗin talauci.

Sannan, da wannan shirin wanda ba wata gwamnatin da ta taɓa tunanin yin sa, shugaban ƙasa ya cancanci yabo da goyon bayan domin cimma maƙasuɗin shirin.

Ina son na faɗa mu ku cewa ina goyon bayan wannan kiran ga shugaban ƙasa na ya mayar da shirin doka kafin ya kammala wa’adin sa. Yin hakan, zai taimaka wajen rage ƙalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Abin takaici ne a ce, mutum ya tashi da safe yana tunanin abin sawa a baki, yadda zai je asibiti ko yadda zai kai yaran sa makaranta, amma wannan shirin ya rage wa mutane waɗannan matsalolin.

Sannan idan akayi doka sannan aka tabbatar da ita, ba gwamnatin da za ta dakatar da ita, sannan ‘yan Najeriya za su cigaba da cin moriyar shirin wanda hakan zai rage matsalar rashin aikin yi.

A cewar sa

Sakon su zai isa ga shugaba Buhari

Gwamna Masari ya tabbatar wa da masu cin gajiyar shirin cewa saƙon su zai isa zuwa ga shugaba Buhari da majalisar wakilai.

Lokaci ya yi da ya kamata ka bayyanawa al’umma wanda zai maye gurbinka – Gwamna ya bukaci shugaba Buhari

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ba jam’iyyar APC shawara akan tsarin ta na karɓa-karɓa

Abiodun yayi nuni da cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar ne zai fito da ɗan takarar da zai jagoranci jam’iyyar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe