Fasinjoji da dama sun yi cirko-cirko ranar Asabar a filin jirgin sama na Murtala Muhammad International Airport da ƙe Legas, bayan an ɗauke wutar lantarki a wani sashin filin jirgin. Jaridar Leadership ta rahoto.
Ana samun matsalar wutar lantarki a Najeriya
Duk da cewa ana fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya a dalilin ɗurƙushewar maɗaukan wutar lantarki na ƙasa wanda hakan ya shafi filayen jiragen sama yayin da lamarin yaƙe ƙara ƙamari a cikin kwanaki ukun da su ka wuce.
Jaridar Leadership ta samu cewa lamarin ya fi ƙamari ne a ɓangaren masu fita daga filin jirgin saman.
Na sha wahala da safennan sosai wurin hawa jirgi. Wutar lantarki ta yi ɓatan dabo. A cewar wani daga cikin fasinjojin.
Sai dai, an bayyana cewa janareton da ke zama madadin wutar lantarki wanda ke samarwa da filin jirgin wuta ne ya lalace.
Eh an samu matsalar wuta. Janareton ɗayan da mu ke amfani da shi ya lalace. A cewar wani ma’aikacin filin jirgin
Ana ƙokarin magance matsalar
Sai dai, wani ma’aikacin filin jirgin ya shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa hukumar kula da jiragen sama ta Najeriya wato (FAAN) tana ƙoƙarin magance matsalar.
Ramadan 2022: Jirgin ƙasan Harami mai matuƙar gudu zai yi safarar sama da fasinjoji 625,000 yayin azumi
Kamar yadda mujallar Saudi gazette ta ruwaito, jirgin kasa na masallatan Makka da Madina mai tsakanin gudu, zaiyi aiki sau hamsin 50 a rana, lokacin azumin Ramadan.
An kaddamar da wannan doka ne domin yin jigilar mutane dubu dari shida da ashirin da biyar 625,000, daga alhazai na gida da wadanda suka zo daga waje, domin gudanar da Umarah a watan na azumi, mai tsarki.
Haramain Hight-speed Railway, wani wata hidima ce ta jigilar mutane a jirgin kasa, wadda ta hada manyan buranen Makka da Madina, masu tsarki, wadda take da tashoshi a, Kinga Abdallah Economic City, KAEC, Jidda Airport wadda take a tsakiyar birnin Jidda.
A fadar wata majiya daga hukumar, tace, jigilar zata karade hanyoyin Makka da Madina ne, zuwa da dawowa, inda zata ratsa ta, babbar cibiyar ta dake SulaymaniyahJidda, da kuma tashar KAEC dake Rabigh.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com