Borno: ‘Yan sanda sun cafke saurayin da ya yiwa tsohuwa mai shekaru 92 fyade

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Borno: ‘Yan sanda sun cafke saurayin da ya yiwa tsohuwa mai shekaru 92 fyade
Yadda mai wankin mota yayi min fyade sannan ya ɗirka min ciki -Yarinya 'yar shekara 11

Hukumar ‘yan sandan jihar Borno, ta cafke wani Zakariya Ya’u, bisa laifin yin fyaɗe ga wata mata mai shekaru 92 a duniya.

An bayyana yadda yayi mata fyaɗe

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Abdu Umar, ya bayyana a wata sanarwa ranar Alhamis 31 ga watan Maris cewa Ya’u ya aikata laifin ne a yankin Mufa “A” na ƙaramar hukumar Askira Uba a jihar. Shafin LIB ya rahoto

A cewar kwamishinan, matar tana zaune kusa da wani kango lokacin da aka wanda ake zargin ya tura ta cikin gidan sannan yayi mata fyaɗe a ranar 24 ga watan Maris.

Ya bayyana cewa matar ta nemi taimako sannan bata da ƙarfin da zata iya kwatar kanta a hannun wanda yake mata fyaɗen, inda ta cigaba da tsala kuka.

Umar ya bayyana cewa wani jikan matar mai suna Usman Haruna, shine ya kama wanda ake zargin ƙuru-ƙuru sannan ya sanar da ‘yan sanda kafin a cafke wanda ake zargin.

Jikan na ta ya kama wanda ake zargin a kan matar wandon sa a ƙwaɓe da kuma laya ɗaure a ƙugunsa

A cewar kwamishinan ‘yan sandan.

Ya amsa laifin sa

Umar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa sannan ana cigaba da gudanar da bincike kafin a miƙa lamarin gaban kotu.

ISIS FYADE : Yadda ‘yan ta’addan ISIS suka yi min fyade har sau 180 – Inji wata yarinya ‘yar Yazidi

Yazidi sunan wata kungiyar addini ce wadda suke zaune a Arewacin Iraq. Abin takaicin shi ne, an takura musu matuka ta yadda suke tserewa domin tsira da rayuwar su.

An karkashe maza da dama, matan aure da yan mata kuma sai ‘yan ta’adda suka kama su lokacin da suka farmaki Sinjar a watan Agustan shekarar 2014. 

Yan kungiyar ta’addan ISIS, sunyi kafar rago ga mutane  ‘yan Yazidi kimanin mutum dubu hamsin 50,000

Mutanen basu da matsera babu abinci babu ruwan sha da zasu rayu. Da yawa daga cikin su sun rasa ransu a kokarin  hawa kan dutsen Sinjar domin tsira. 

Kamar yadda aka fada a baya, an karkashe maza da dama an kuma kama matan aure da yan mata. Wadannan matan an sanya su a kangin wahala iri-iri. Suna ganin muzanci karara, inda ake cin zarafin su ta fuakar lalata da su. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Rubuta Sharhi