24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

An kama wasu matasa 3 sun yanke kan wani mutum a jihar Gombe

LabaraiAn kama wasu matasa 3 sun yanke kan wani mutum a jihar Gombe

 Rundunar yan sanda ta jihar Gwambe, ta cafke matasa uku 3 saboda zargin samun su kan mutum, sabon yanka.


 Matasan da ake zargin da suka hada da Yale dan shekara 27, Baba Muhammadu dan shekara 24 da kuma Aminu Salisu, dan shekara 22, yan kauyen Dinawa, dake karamar hukumar Kwami ta jihar Gombe, anyi baje kolin su ne a shalkwatar yan sandan jihar Gombe, domin zargin su da hadin baki wajen mallakar wani kan mutum da aka yanke bada dadewa ba. 


Kwamashinan yan sanda Ishola Babaita, ya bayyana cewa an kama masu laifin su uku ne, ranar Litinin 30 ga wata, biyo bayan samun muhimman bayanai. 

matasa
An kama wasu matasa 3 sun yanke kan wani mutum a jihar Gombe

Yadda matasan suka aikata laifin

Yace, kwarya-kwaryan bincike da aka gabatar, ya bayyana cewa :

masu laifin, sun haka kabari ne da daddare, inda suka yanke kan wani mamaci, wanda aka sakaye sunan sa, wanda aka binne shi a ranar 28 ga watan Maris, a makabartar kauyen Dinawa. 

A fadar sa, matasan masu laifin har ilayau,


Kwamashina Baita din ya kara da cewa, kokarin gano wannan kan matar da suka yi ikirari yayi nisa, inda su kuma aka garzaya dasu babbar cibiyar binciken manyan laifuka ta jahar , domin bin kwakkwafi akan laifin da kuma gurfanar da su a gaban sharia.

sun sake tabbatarda cewa sun taba tona kabarin wata mata ma, a dai wannan makabartar ta Dinawa, inda ita ma suka yanke kanta. 

Wani makamancin laifin da wasu suka aikata

 Haka kuma, an kama wani Aliyu Musa Nagangarawa dan shekara 20 dake kauyen DabanMagarya a karamar hukumar Balanga dake jihar Gwambe, da laifin kisan dan kanin baban sa. 


Baita din yace, jami’an yan sanda dake a can Balanga din ne suka kama mai laifin, a ranar 23 ga watan Maris, bayan ya dabawa dan uwan nasa mai suna Dahiru Mukhtar,  wuka a wuya Saboda sabani da suka samu akan wando. 


Yan sanda sun tabbatarda cewa, mai laifin ya amsa laifin sa, kuma za’a gurfanar dashi a gaban kotu yayin da aka kammala bincike. 


Sannan kuma, hukumar ta sake yin baje kolin wasu mutum 12, da ake tuhumar su da laifuka daban-daban, da suka hada da, fyade, sata, hadin baki domin aikata barna, mallakar makamai ba bisa kaida ba, da kuma, balle gidajen mutane domin sata. 


Hukumar yan sanda, tace duk laifukan ana gudanar da bincike akan su, kuma za’a gurfanar da masu laifukan a gaban kotu, domin girbar abin da suka shuka.

‘Yan sanda sun kama matashi da laifin kashe mahaifiyar sa

A Jiya Laraba ne ‘yan sanda suka yi  atisaye, inda suka cafke mutane takwas masu laifi daban-daban a jihar Gwambe. 
Daya daga cikin masu laifin mai suna Garba Abubakar dan shekara 26, ana zargin ya kashe mahaifiyarsa mai suna Salamatu Abubakar, yar shekara 45, ta hanyar shake mata wuya. 

Jawabin kwamashinan yan sanda a kan laifukan


Kwamashinan ‘yan sanda Ishola Babaita ya bayyana cewa,

” Mai laifin ya kashe mahaifiyarsa ne saboda tana yawan yi masa nasiha da ya bar halayyar shaye-shayen kwayoyi. An garzaya da ita babban asibitin Kumo, inda likita ya tabbatar da mutuwarta. 

” Ina shawartar iyaye da su sanya kyakkyawar kula a kan ‘yayan su, su kuma tabbatar ‘ya’yan nasu basu fada cikin mummunar dabi’ar shaye-shayen ba. Abin bakin ciki, wannan mata danta na cikin ta  ya hallaka ta wannan shi ne mummunan tasirin miyagun kwayoyi”.

Ya fada.

An kama wani mutumi da laifi na daban


Haka kuma, wani guda daga cikin masu laifin, Adamu Lawal, dan shekara 53, an kama shi ne akan zargin yin fyade ga wata yarinya ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara 10 wacce ta kasance tana kai masa abincin dabbobi. 

.” Mai laifin ya yi amfani da wannan damar inda yayi amfani da karfi wajen lalata da yarinyar “A fadar  Kwamishina Babaita.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe