24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wata matashiya ta bayyana Yadda mahaifinta ya yi mata ciki,kuma ya dinga dirka mata kwayoyi don cikin ya zube

LabaraiWata matashiya ta bayyana Yadda mahaifinta ya yi mata ciki,kuma ya dinga dirka mata kwayoyi don cikin ya zube
Kotu
Wata matashiya ta bayyana Yadda mahaifinta ya yi mata ciki,kuma ya dinga dirka mata kwayoyi don cikin ya zube

Ta zayyanawa kotu yadda mahaifinta yake lalata da ita har ya dirka mata ciki

Wata matashiya ‘yar kimanin shekara 20 wacce aka sakaya sunan ta a ranar Alhamis ta shaida wa wata Kotu a garin Ikeja yadda mahaifinta, Akin Isaac, ya yi mata ciki tare da zubar da cikin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa, matashiyar,wanda mai gabatar da kara na jihar, Y. A. Alebiosu ya jagoranci karar a gaban kotu, ta ce tafara zama da kakar ta ne kafin daga baya ta dawo hannun mahaifinta.

Tun tana shekaru 17 ya fara lalata da ita

Matashiyar ta bayyana cewa mahaifinta ya yi mata fyade tun tana shekara 17 lokacin kullen dokar COVID-19 na shekarar 2020 a gidansu da ke Alapere, Legas.

Ta ce mahaifinta ya bukaci ta dawo hannun sa da zama a shekarar 2019 domin ta sami damar cigaba da zuwa makarantar sakandare da kuma ba shi damar kula da ita yadda ya kamata.

Matashiyar ta ce mahaifinta ya kasance yana da mata biyu abin mamaki yafara kai hannu jikinta.

Na ji tsoro sosai,har na rokeshi ya yi hakuri ya kyaleni, amma ya je ya sayo dorina ya ajiye a kan tebur, inda ya yi amfani da ita ya yi ta jibgata saboda kawai ya yi lalata da ni.

Ya yi barazanar zai kashe ni idan har na fadawa wani. Ina da shekara 17 a lokacin. Ina aji Uku karamar sakandire, na kasance mutum mai son wake wake amma lokaci daya na chanza.

Wata rana da safe na je na sameshi na rokeshi cewar ba na son rayuwa na ya lalace amma ya yi biris da roƙona ya cigaba da aikata masha ansa. Kodaya gama na kasa fita,” inji ta.

Matashiyar ta cigaba da zayyanawa kotun cewar mahaifinta karfi da yaji ya hana ta zuwa coci.

Na kasance ina zuwa cocin C&S amma Ya hana ni zuwa sai faston mu ya zo ya roƙe shi ya bar in cigaba da zuwa cocin.
“Mako na biyu da ya zagayo ranar lahadi,na je coci, amma sai ya sake dakatar da ni ya ce daga yanzu in dinga zuwa cocin Redeemed ni kuma na ce masa ba na son zuwa can
.

Mahaifina ya yi nasarar kwace wayata, ya karya layin wayana saboda kawai kar inyi magana da ɗan’uwana ɗan kimanin shekara 27 wanda shikadai ne nake iya gayawa damuwa,ta.

“Ya taba duka na karfen tauraron dan Adam na Gotv, har sai da wasu makwabta suka bukaci in gudu inzo in zauna da su yayin da wasu ke tsoronsa saboda shi dan OPC ne,” in ji matashiyar.

Ta shaida wa kotun cewa rashin ganin al’adar ta shiya sa ta fahimci cewar tana da ciki, Inda mahaifin nata ya yi yunkurin zubar da ciki ta hanyar bata magunguna da allurai amma abin ko,gezau.

sai da aka yi mini allura 15 saboda kawai cikin ya zube. Ya sayi magani, ya sayi allura amma duk a banza, Wata ma’aikaciyar jinya ta tambaye ni waye ya yi min ciki, amma na kasa gaya furta mata babana ne.

Daga baya ya kai ni wani wuri mai duhun gaske inda ya yi nasarar zubar da cikin a wurin,” in ji ta.

Ta cigaba da shaidawa kotun cewa mahaifin nata ya yi yunkurin sake saduwa da ita a lokacin da take barci a watan Yuli, 2020, bayan cikin da ya yi mata na farko ya zube, amma ta ki, wanda hakan ya sa makwabta suka shiga tsakani.

A daren nan, ya fara dukana, sai makwabta suka shiga tsakani, sai ya ce musu ni diyarsa ce, kuma shi yake da damar yi mata duk abinda ya so, har ma ya ce idan ya ga dama zai iya kashe ni saboda ni diyarsa ce. ,” in ji ta.

Ma’aikaciyar jin dadin jama’a ta ce ta je ofishin ‘yan sanda kuma wata ‘yar sanda ta raka ta zuwa gidan yarinyar.

Ta kara da cewa daga baya ne suka kai wanda ya tsira zuwa ofishin ‘yan sanda inda suka dauki bayananta, kuma a ofishin mahaifinta ya zo suka kama shi.

“Lokacin da muka isa ofishin, ta ce mahaifinta ya taba yi mata ciki kuma ya kai ta wani wuri domin ya zubar da cikin,” kamar yadda aikin zamantakewa ya shaida wa kotu.

Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo  ya dage sauraron karar har zuwa ranar 13 ga Afrilu domin ci gaba da shari’ar.

Budurwa mai shekaru 50 da tayi aure ta haifa ‘yan uku bayan tayi shekaru 25 da aure

Bayan shekaru 25 da aure tar da fama da rashin haihuwa, wasu ma’aurata a Najeriya yanzu suna alfahari da iyayen ‘ya’yansu yayin da suka yi maraba da wasu ‘yan uku.
Sabon mahaifin, Deacon Michael Nwankwo, ya bayyana a cikin wata hira cewa bai taba tunanin zasu jira tsawon lokaci ba su haifi ‘ya’yansu.
A cewarsa, ya yi aure yana dan shekara 26 don kawai ‘ya’yansa su girma tare da shi amma ba haka lamarin yake ba.
Ma’auratan sun yi aure a cikin shekarun su ashirin amma ba su yi nasara wajen samun ‘ya’yansu ba duk da binciken duk wani zaɓi na halal, ciki har da yin IVF. Ma’auratan sun yi aure a matsayin saurayi budurwa

Da yake magana da jaridar The Punch a wata hira, sabon mahaifin ‘ya’ya uku mai suna Deacon Michael Nwankwo ya ce bai taba tunanin ‘ya’yansu za su zo sama da shekaru ashirin da aure ba.
Sabuwar mahaifiyar har yanzu tana son karin yara A cewar dan kasuwar Legas mai _shekaru 52, ya auri matar sa yana da shekara 26 a kokarinsa na haihuwa da wuri kuma su girma tare da su.

“…Ni mutum ne mai tsananin sha’awar ’ya’ya, kuma burina na yi aure lokacin da na yi shi ne in haifi ’ya’ya na ga ’ya’yana da na girma tare, ba zan iya tunanin zai kai matsayin da zan samu ba don jira shekaru 25.

“A cikin watanni biyun farkon aurenmu, matata ta samu juna biyu, kuma abin takaici, saboda rashin kwarewa muka yi tafiya zuwa Ghana kuma ta zubar da jaririn. Daga nan sai kawai ya hau zuwa ƙasa, tafiya ba abu mai sauƙi ba ne.”_ Ya ce: Duk da haka, ya gode wa Allah da ya sa ya zama uba.

A nata bangaren, sabuwar mahaifiyar, Victoria Nwankwo, mai shekaru 50, ta gode wa Allah da ya ba ta mu’ujiza, inda ta bayyana cewa ta daina ganin al’ada lokacin da ciki ya zo.
Victoria wacce ta daura auren a matsayin budurwa tana da shekaru 24 ta ce tana fatan samun karin yara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe