24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Koda lokacin yakin Basasa, yanayin Najeriya bai tabarbare haka ba- Inji Chief Joop Berkhout baturen kasar Netherlands

LabaraiKoda lokacin yakin Basasa, yanayin Najeriya bai tabarbare haka ba- Inji Chief Joop Berkhout baturen kasar Netherlands


Wani baturen kasar Netherlands, wanda ya zauna a Najeriya tsawon shekara 55, mai suna Chief Joop Berkhout, yayi tur da Allah wadai, da harin da yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, a jihar ta Kaduna. 


Baturen dan shekara 92, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin gida a gareshi, yace yanayin Najeriya a lokacin yakin basasa,  yafi kyawu nesa ba kusa ba idan aka kwatanta da halin da yan kasar suke fuskanta a yanzu. 


Ya bayyana hakan ne yayin da jaridar Daily Trust take hira da shi, a wajen bikin cika shekara 92 da yayi a ranar Talata a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo. 

najeriya
Chief Joop Berkhout baturen kasar Netherlands


Ya kara da cewa, “

Najeriya bata sami kyakkyawan canji ba. Abin da ya faru yan kwanakin da suka wuce, ba karamin mummunan abu bane. Babu wata kasa a duniya inda ake kai hari tashar jirgin sama, ko jirgin kasa, yanzu abun ban tsoro ne, ka yi tafiya zuwa Kaduna. Shima filin  jirgin Kaduna an kulle shi saboda tsaro. 


“Jirgin kasan ma an dakatar da shi daga Abuja zuwa Kaduna. Koda lokacin yakin basasa yafi yanayin da ake ciki a yanzu, saboda a wancan lokacin zaka iya yawo duk inda kake so a Najeriya. Zan iya barin Ibadan tun karfe 6 na safe inje ko ina a mota, kuma ina yin hakan dare da rana”


Daga karshe ya shawarci yan Nageriya da dinga haifar yayan da suka tabbatar zasu iya kula da tarbiyyar su, saboda shi a ganin sa, yawan mutane da talauci sune suka  jawo halin da Najeriya ke ciki a yau. 

Kwanaki kadan da isowar Tsohon Bature Kano, Wata budurwa ta yi wufff da shi

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta wallafa hotuna da bidiyoyin shagalin bikinta da wani tsohon bature bayan kwanaki kadan da zuwansa Najeriya.
Bidiyon ya nuna yadda su ka yi bikinsu sanye da sutturun gargajiya tare da wasu kawaye da ‘yan uwan budurwar.
‘Yan Najeriya da dama sun dinga cece-kuce akan bidiyon wanda ya nuna ita da tsohon angon nata cike da farin ciki.

Budurwar ta nuna tsabar murnarta kamar yadda Linda Ikeji ta kara wallafawa inda ta ce budurwar na matukar farin cikin auren babban abokinta.
Akwai wani bidiyo na daban da ya nuna yadda su ka rungume juna bayan isowar baturen Najeriya.
Dattijon ya nuna farincikinsa a bidiyon bayan haduwarsa da masoyiyar tasa.
Bidiyon ya nuna yadda su ka yi bikin a saukake sannan akwai inda baturen ya durkusa ya sa wa matar tashi zobe a hannunta.
Har ila yau akwai wani bidiyon da aka hada musu na hotunan da su ka dauka lokacin shagalin bikin wanda farin cikinsu ba ya misaltuwa.
Budurwar ta nuna zobenta cike da alfahari da wasu kudade na kasar waje.

Yadda tsohon mijin Momi Gombe zai yi wufff da Nana Izzar so, abokiyar sana’arta

Cikin kwanakin nan hotuna su ka bayyana na wani fitaccen mawakin Kannywood, Adam M Fasaha, wanda tsohon miji ne ga Jaruma Momi Gombe da wata jarumar ta daban, Minal Ahmad wacce ta fito a matsayin Nana cikin shirin Izzar so mai dogon zango.
Shirin Izzar so ya sa ta yi matukar farin jini da shahara inda tun daga nan ta samu karbuwa a masana’antar Kannywood don akwai sababin shirye-shirye kamar ‘Sarki Goma’ da sauransu da ta taka babbar rawa a cikin su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe