‘Yan sanda sun cafke wasu mutum 3 masu tono ƙaburburan mutane a jihar Gombe

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing ‘Yan sanda sun cafke wasu mutum 3 masu tono ƙaburburan mutane a jihar Gombe

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Gombe ta cafke wasu mutum uku da ake zargim cewa sun ƙware wajen satar sassan jikin gawarwaki a maƙabartu a jihar, bayan an samu kawunan mutane a hannun su. Jaridar Punch ta rahoto

An bayyana sunayen su

Waɗanda ake zargin sun haɗa da: Yale Saleh, mai shekaru 27, Baba Muhammadu, mai shekaru 24, da kuma Aminu Salisu, mai shekaru 22, dukkanin su daga ƙauyen Dinawa a ƙaramar hukumar Kwami ta jihar Gombe.

‘Yan sanda sun samu nasara akan su

A cewar kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Gombe, Mahid Abubakar, jami’an hukumar sun samu nasarar ƙwace gangar kan mutum ɗaya daga cikin biyun da su ka tono daga ƙabarin su.


Abubakar ya ce:

Bisa samun gamsassun bayanai, an cafke waɗanda ake zargin ɗauke da kan mutum. A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun tona kabari sannan su ka cire kan wani Abdullahi Mohammed wanda aka binne a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 a maƙabartar ƙauyen Dinawa.

Waɗanda ake zargin kuma sun ƙara amsa cewa sun tona kabarin wata mata wacce baa bayyana sunan ta ba a maƙabartar ta ƙauyen Dinawa sannan su ka cire mata kai. An miƙa lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka domin cigaba da gudanar da bincike.

Abubakar ya buƙaci jama’a da su cigaba da bayar da muhimman bayanai domin ganin an kawar da aikata munanan laifuka a jihar.

Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani yaro mai shekaru 18, Abdulsamad Suleiman, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, Gwale, cikin birnin Kano, tare da abokin harƙallar sa Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, bisa zargin hallaka wata matar aure. Jaridar Punch ta rahoto

Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Abdullahi Haruna, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya bayyana cewa:

‘’A ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, mun karɓi rahoto daga wani mazaunin Danbare Quarters, ƙaramar hukumar Kumbotso, ta jihar Kano, cewa a wannan ranar da misalin ƙarfe 8 na dare bayan ya dawo gida daga wajen aikin sa, ya samu matarsa Rukayya Jamilu mai shekaru 21, kwance cikin jini.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi