29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

An ɗaura auren jaruma Nafisa Ishak wacce ta zagi Sheikh Aminu Daurawa

LabaraiKannywoodAn ɗaura auren jaruma Nafisa Ishak wacce ta zagi Sheikh Aminu Daurawa

Jarumar Kannywood Nafisa Ishak ta angwance ita da mijinta.

An wallafa bidiyon auren Nafisa Ishak

A wani faifan bidiyo da tashar Duniyar Kannywood ta wallafa na bikin jaruma Nafisa Ishak, an nuna mijin da ta aura suna nunawa junan su shaukin ƙauna.

Haka kuma a cikin bidiyon an nuna wani wuri inda anan ne aka ɗaura auran jarumar da mijin na ta.

Ita kanta jaruma Nafisa Ishak ta wallafa bidiyon ta angon na ta a shafin ta na Tiktok da Instagram tana faɗin “Alhamdulillah.

Nafisa Ishak
An ɗaura auren jaruma Nafisa Ishak wacce ta zagi Sheikh Aminu Daurawa

Ta goge duk wata wallafar da tayi a baya

Sannan kuma jarumar ta goge duk wata wallafa da tayi a baya inda ta bar kawai na ɗaurin auren da kuma wanda ake kai ta ɗakin miji.

A kwanakin baya dai Nafisa ta tsinci kanta cikin wata taƙaddama bayan tayi raddi ga shahararren malamin addinin nan Sheikh Aminu Daurawa.

Raddin da ta yi ga malamin ya sanya ta sha suka a wajen mutane da dama wanda hakan ya sanya dole ta yi wani bidiyo inda ta bayar da hakuri.

Muna yi mata fatan alkhairi da fatan Allah ya bada zaman lafiya.

Sheikh Daurawa – Auren Wuf da ake yi ba shi da wata matsala a Musulunci

Shahararren Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano, wanda ya karade lungu da sako na Arewa dama Najeriya baki daya, Sheikh Aminu Ibrahim, wanda aka fi sani da Sheikh Daurawa, ya yi karin haske dangane daa auren ‘Wuf’ da ake yi a wannan lokacin.

Malamin ya tabbatar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi 3 ga watan Oktobar shekarar 2021.

Kalmar ta “Auren Wuf” ta fito ne sakamakon aure da ake yi namiji ya auri matar da ta fi shi yawan shekaru, musamman ma idan matar tana da kudi, ko kuma sabanin haka, wato mata ta auri namiji wanda ya ninka ta sau biyu ko sau uku a shekaru.

A bayanin da Sheikh Daurawa ya yi, wanda ya rike mukamin tsohon shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, ya ce ko a addinance babu wani laifi dan mace tayi wuf da saurayin da ta girma, ko kuma dattijo ya auri budurwar da ya ninka a shekaru.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe