22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Yahaya Bello ya bayyana wani boyayyen abu game da Bola Tinubu yayin da ya cika shekara 70 a duniya

LabaraiYahaya Bello ya bayyana wani boyayyen abu game da Bola Tinubu yayin da ya cika shekara 70 a duniya
d29c781a2bbfb2df
Yahaya Bello ya bayyana wani boyayyen abu game da Bola Tinubu yayin da ya cika shekara 70 a duniya

Gwamna yahya Bello ya taya Sanata Ahmad Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya taya Sanata Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 70 a ranar , Talata, 29 ga watan Maris. lRahotan nin sun bayyana cewa gwamnan ya bayyana Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin hazikin shugaba wanda ya chanchanci yabo.Gwamna Bello wanda sakon ya fito ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Muhammed Onogwu, ya ce tsohon Tinubu ya taka babbar rawa a tarihin dimokuradiyya da siyasar Najeriya.

Ya yabawa Tinubu

Ya yaba da irin rawar da Sanata Tinubu ya taka a matsayin sa na uba kuma jagorar kafa jam’iyyar APC tare da Shugaba Muhammadu Buhari da sauran masu kishin kasa.
Gwamna Bello ya kara da cewa a ko da yaushe Sanata Tinubu ya kasance shugaba nagari a fagen siyasar Najeriya. Sannan ya yi masa fatan Allah ya karo shekaru masu albarka cikin koshin lafiya, Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya ba shi tsawon rai domin ya ci gaba da jajircewa wajen tallafawa matasa.


In har Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, zan bar Najeriya, Jagoran PDP, Bode George
Jagoran jam’iyyar PDP, kuma tsohon shugaban hukumar kula da madatsun ruwa, Bode George ya ce zaiyi wa Najeriya kaura idan Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya, LIB ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da manema labarai a Legas ranar Asabar 19 ga watan Maris, George ya ce, Tinubu zai tabbatar da iyalinsa sun mamaye mukamai masu gwabi idan ya zama shugaban kasa, inda ya kara da cewa tsohon gwamnan bai tabuka aikin da ya taka kara ya karya ba da har ya cancanci kujerar.
Cewarsa;

“Ina farin ciki da rattaba hannun da shugaban kasa yayi akan sabuwar dokar zabe. Idan har ko ta yaya ne ya shiga fadar shugaban kasa (yana nufin Tinubu), bazan ci gaba da zama a kasar nan ba.

“Kuma ba da wasa nake ba. Zan iya tafiya Ghana, in yi zama na a can, in zuro muku na mujiya daga nesa. Zaku ga abunda zai faru.

“Wannan mai juya jihar Legas din zai samo wasu masu yankar aljihu daga wani wurin da zasu yi awon gaba da kudaden ku. Matar sa zata zama shugaban majalisar dattawa. Dan shi kuma zai zama gwamnan Legas. Ita kuma ‘yar sa zata zama sarauniyar Najeriya.

“Me yayi don tabbatar da ya cancanci wani ya girmamashi a kasar nan?

“Babu abunda yayi. Hakikanin gaskiya, diyar ‘yar uwata ta kira mi. Ta ce ‘wasu mutanensu na yamadidi cewa yana bani ‘yan kudade. Wai Bola yana bani kudi’.
“Ya kawo kudin ya gani. Zan ce mai ya biyoni Lagos Island – mutane na cikin yunwa a can. A can na taso – a Lagos Island.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe