27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Idan ‘yan Najeriya suka yi wasa, Buhari zai ci gaba da mulkarsu har abada, Sule Lamido

LabaraiIdan 'yan Najeriya suka yi wasa, Buhari zai ci gaba da mulkarsu har abada, Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya ce “Idan ƴan Najeriya sun so su bar Buhari ya cigaba da mulki har abada.”

Ya bayyana hakan ne yayin zantawa da BBC Hausa a kwanakin baya.

Za su gyara ɓarnar APC

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa:

Jam’iyya APC annoba ce a Najeriya, ta janyo masifu marasa iyaka, babban aiki ne gyara barnar da APC ta tafka, ta janyo gaba tsakanin ɗa da uwa, wa da ƙani, gari da gari, dangi da dangi, addini da addini da kuma kudu da arewa.”

Amma idan an buƙaci mu bayar da tami gudunmawar, zamu bayar da yardar Ubangiji,” a cewarsa.

BBC Hausa ta tuntuɓi kakakin fadar shugaban ƙasar Najeriya Garba Shehu, amma ya ce ba ta tasa suke ba, daga baya za su mayar masa da martani.

Sule Lamiɗo
Idan ‘yan Najeriya suka yi wasa, Buhari zai ci gaba da mulkarsu har abada, Sule Lamido

An muzanta Sule Lamiɗo saboda Buhari

Sule Lamiɗo ya ce, saboda yadda ƴan Najeriya ke son ganin Buhari ya ɗare madafun iko, “an kira mu da arna, an kira mu da kirista, an ce ba ma kaunar musulunci, ba ma kaunar arewa, babu abunda ba a ce mana ba, an kira mu da ƴaƴanmu ɓarayi.

An ce Buhari waliyyi ne, ma’asumi ne, da dai sauran su, an ci fuskar mu

Ya ce:

idan har yanzu ƴan Najeriya basu farka daga nannauyan baccin da suke ba na goyawa APC baya, to sai sun dawwama a mulkin Buhari har abada.”

Ya soki jam’iyyar APC

Babban ginshiƙin jam’iyyar adawa ta ƙasa ta jam’iyyar PDP dai ya zargi APC da rusa dukkan tushen da aka gina ƙasar a kai don tabbatar da haɓakarta.

Kamar yadda ya faɗa, hakan ya sa PDP fafutukar ganin ta karɓi mulki don ceto Najeriya daga ƙangin da ta ke ciki.

Tsohon gwamnan Jigawan na cikin mutanen farko da suka kafa jam’iyyar PDP tun shekarar 1998, sannan yayin tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce PDP ce kaɗai jam’iyyar da zata fidda kasar daga ƙangin da take ciki.

Manyan jam’iyyar PDP sun tsayar da Sule Lamido a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023

Manyan ‘yan babbar jam’iyyar adawa ta PDP na jihar Jigawa sun nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido a matsayin dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Manyan jam’iyyar ta PDP da suka fito daga garin Bamaina dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu dake jihar Jigawa, a ranar 31 ga watan Agusta, sun bayyana cewa tsohon gwamnan yana da duka wata kwarewa da ta dace ya rike kujerar ta shugaban kasa, rahoton PM News.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe