27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Allah ya isa tsakaninmu da Buhari da muƙarrabansa, Ɗan gwagwarmaya Sada Suleiman Usman

LabaraiAllah ya isa tsakaninmu da Buhari da muƙarrabansa, Ɗan gwagwarmaya Sada Suleiman Usman

Wani fitaccen dan gwagwarmaya, Sada Suleiman Usman ya yi wata wallafa a shafinsa na Facebook wacce ta dauki hankalin jama’a da dama.

Ya soki shugaba Buhari

Kamar yadda ya ce, Allah ya isa tsakaninsu da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma makusantansa wadanda suka gaza fada masa gaskiya.

Sada ya yi wannan wallafar ne cike da alhini, kwanaki kadan bayan wani kazamin farmaki da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasa a garin Kaduna.

Harin nasu ya ritsa da fasinjoji 970 kamar yadda majiyoyi suka shaida, kuma a cikin su mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu suka raunana.

Duk da dai akwai wadanda suka tsira amma hankalin mutane da dama ya tashi kasancewar an dade rabon da a ji makamancin wannan harin.

Buhari
Allah ya isa tsakaninmu da Buhari da muƙarrabansa, Ɗan gwagwarmaya Sada Suleiman Usman

Hakan ya sanya Sada ya kada baki ya ce:

Allah ya isa tsakaninmu da Buhari da mukarrabansa.”

Mutane sun bayyana ra’ayoyin su

Wallafar ta dauki hankali kwarai, don dubbannin mutane sun dinga tsokaci karkashinta, wasu suna yaba masa yayin da wasu suke kalubalantarsa.

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin wallafar:

Wani Yamai Muhammad ya ce:

Kayi haquri Sada, zan fada maka gaskiya mai daci yau. Duk matsalolin da suke faruwa yanzu sun faru kafin za6en 2019, amma haka kuka sake za6en Buhari, maimakon a gwada canzashi da Atiku shima aga kamun ludayinsa.

Wani Mustapha Zakiria ya ce:

Daga ranar da Buhari ya tafi, daga lokacin za ku gane cewa ba wai laifinsa ba ne.”

Ustazu Mubarak Musa ya ce:

Allah Yana nan a madakata.
Kuma wallahi shine mafi adalcin masu adalci. Shi yasa mu ke da yaƙinin zai mana adalci akan masu ƙaryar adalci

Activist-Isma’eel S Jauro ya ce:

Kashe-kashen da akayi a Jihar Katsina Tabbaas abin a jawa Shugabannin mu Allah ya isa ne.”

Hussaini M Ahmad Yelwa ya ce:

Wlh kuwa sai Allah ya yi mana sakayya, domin sun cucemu.”

Idan ‘yan Najeriya suka yi wasa, Buhari zai ci gaba da mulkarsu har abada, Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya ce “Idan ƴan Najeriya sun so su bar Buhari ya cigaba da mulki har abada.”

Ya bayyana hakan ne yayin zantawa da BBC Hausa a kwanakin baya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe