27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Kano: Yadda jami’an tsaro suka yi ram da yaro dan shekara 17 bayan ya kwakule wa Almajiri ido saboda asiri

LabaraiKano: Yadda jami’an tsaro suka yi ram da yaro dan shekara 17 bayan ya kwakule wa Almajiri ido saboda asiri

Wani ƙaramin yaro mai suna Isah Hassan wanda aka fi sani da suna Shahidai mai shekaru 17 ya shiga hannun hukuma bisa cire idanun wani yaro Mustapha Yunusa, mai shekaru 12 a unguwar Dan Tsinke cikin ƙaramar hukumar Tarauni ta jihar Kano. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Yaron ya bayyana wanda ya sanya shi aikin

Shahidai ya ƙwaƙwule idanun Mustapha ne bisa umurnin wata bokanya mai shekaru 107 domin yi masa laƙanin ɓacewa.

Sai dai, Sayyada Furera Abubakar, ta musanta zargin da ake mata, inda ta ke cewa ƙoƙarin taimaka masa da maganin gargajiya kawai ta ke yi.

“Ni mai bada maganin garjajiya ce kawai. Ƙarya ya ke min. Ina da sama jikoki 50 kuma ban cire musu idanun su ba. Meyasa zan yi haka?

Mahaifin yaron yayi magana kan lamarin

Da yake magana, mahaifin yaron, Dahiru Ahmad, ya bayyana cewa ya kai yaron wajen aminin sa, Malam Arma, domin karatu a Dan Tsinke.

An kira ni inda ake cemin ɗa na yana asibitin Murtala. Bayan na isa, an gaya min cewa wasu ɓata gari su tare shi sannan su ka ƙwaƙule masa ido. Muna godiya ga Allah tare da taimakon ‘yan sanda da ma’aikatan lafiya, sun yi ƙoƙari sosai sannan yaron ya samu sauƙi yanzu inda ya ke gani da ido ɗaya.

Jiya da misalin ƙarfe 1 na dare, an gaya min cewa yaron da ya cirewa ɗa na ido an cafke shi kuma ya amsa cewa ya aikata laifin.

An bayyana yadda aka yi ram da yaron

Ali Abdulhamid shine kwamandan ‘yan sakai na Dan Tsinke waɗanda su ka cafke wanda ake zargin. Ya bayyana cewa:

Mun cafƙe Shahidai a iyakar Kumbotso da Tarauni. Ya ƙwaƙule idon yaron sati biyu da su ka wuce, cikin ikon ubangiji mun kama shi yana ƙoƙarin cire wani idon.

Ɗaya daga cikin jami’an mu ya kawo mana rahoton cewa wani yaro yana son aikata laifi sannan yana buƙatar haɗin kan sa wajen aikata laifin. Ya bayyana mana yanayin laifin inda mu ka ce masa da ya nuna masa kamar yana tare da shi.

Daga nan, ya buƙace shi da ya taho da wuƙar da zai yi amfani da ita wajen ƙwaƙule idon. Mun shaida masa cewa ya kai ma wuƙar sannan mu ka biyo su zuwa wurin inda mu ka samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Shahidai ya amsa cewa ya aikata laifin da ake zargin sa da shi.

Da ya ke magana dangane da lamarin, kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa hukumar za ta gudanar da bincike kan lamarin bisa yadda ya dace.

Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani yaro mai shekaru 18, Abdulsamad Suleiman, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, Gwale, cikin birnin Kano, tare da abokin harƙallar sa Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, bisa zargin hallaka wata matar aure. Jaridar Punch ta rahoto

Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Abdullahi Haruna, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya bayyana cewa:

A ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, mun karɓi rahoto daga wani mazaunin Danbare Quarters, ƙaramar hukumar Kumbotso, ta jihar Kano, cewa a wannan ranar da misalin ƙarfe 8 na dare bayan ya dawo gida daga wajen aikin sa, ya samu matarsa Rukayya Jamilu mai shekaru 21, kwance cikin jini. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe