22.5 C
Abuja
Friday, December 2, 2022

Kwanaki kadan bayan bayyana sabon shugaban jam’iyyar APC, manyan ministocin Buhari sun fara shirin barin jam’iyyar

LabaraiKwanaki kadan bayan bayyana sabon shugaban jam'iyyar APC, manyan ministocin Buhari sun fara shirin barin jam'iyyar
3c041179a29419bd
Kwanaki kadan bayan bayyana sabon shugaban jam’iyyar APC, manyan ministocin Buhari sun fara shirin barin jam’iyyar

Duk da anyi zaben shugaban jam’iyya har yanzu akwai ‘yan tashin tashina da ke tashi a jam’iyyar ta APC

Har yanzu rikicin da ke mamaye da jam’iyyar All Progressives Congress bai lafa ba a akalla akwai kimanin jihohi 12 da ke fuskantar tashin tashina duk da an gudanar da zaben shugaban jam’iyya da kuma kiranye da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi akan hadin kai. Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamitin sulhu karkashin jagoranci Sanata Abdullahi Adamu wanda yanzu shi ne ya yi nasarar dalewa shugabancin jam’iyyar bai mika cikakken rahotonsa ba rahoton wucin gadi ne kawai aka mika wa jam’iyyar ta APC.
Idan ba a manta ba akwai shari’o’i da suka fito daga jam’iyyar ta Apc dai-dai har guda 208 da ake ci gaba sauraron su a kotu a sassa daban-daban na fadin kasar.
Sai dai kuma duk da sulhun da aka samu daga na shar’o’i da ke cikin jam’iyyar , wasu da dama wadanda ba suyi nasarar kujera ba sun fara ficewa daga jam’iyyar, yayin da wasu kuma suka shiga tattaunawa da jam’iyyar PDP.

Wasu daha cikin jihohi sun dage tuttar jam’iyya daga sakateriya

Jihar kwara

A jihar kwara an sami nayanin cewa mambobin jam’iyyar APC karkashin jagorancin ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammed,sun dage tuttar jam’iyyAR daga sakatariyar su.An sami wannan labarin ne a waja ziyara da aka kai sakatariyar mai lamba Adireshi 26 Abdulrazak Road,flower garden, GRA,Ilorin,an ga mambobin sun fice daga wurin. Da majalisar dokoki jihar mai wakiltar mazabarOjomu\Balogun a karamar hukumar Offa,saheed Popoola,wanda ya kasance jigo ne a tawagar Lai Muhammed,ya bayyana ra’ayin sa na son sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party wanda ya bayyana hakan ne a taron zaurenn majalisa.

Jihar Osun

A jihar Osun, Abiodun Agboola, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC mai dan tawagar ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce ‘ya’yan kungiyar na,nan na jiran kotu ta yanke hukunci kan wani batu da ta kafa na kalubalantar cancantar Gwamna Gboyega Oyetola, wanda yanzu haka shari’ar ke gaban kotu a Abuja.
Ya ce: “Ba bu inda zamu je muna nan a matsayin mambobin jam’iyyar APC ba gudu ba ja da baya. Mu na nan a matsayin ‘yan ‘yan jam’iyyar APC. An gama babban taron kas,a an kaddamar da sababin shugabanni kuma an rantsar da su.”

Babban taron APC: Jerin sunayen ‘yan takarar shugaba Buhari da gwamnoni su ka sauya
Wasu daga cikin ‘yan takarar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke marawa baya sun sha kashi a wajen babban zaɓen jam’iyyar APC na ƙasa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An sauya ‘yan takarar shugaba Buhari
A wajen babban taron jam’iyyar wanda ya gudana a dandalin Eagle Square, ranar Asabar, aƙalla huɗu daga cikin ‘yan takarar da ke da goyon bayan shugaba Buhari kafin taron, aka sauya.

Sai dai sanata Abdullahi Adamu, wanda shine na farko a cikin ‘yan takarar da da shugaba Buhari ya zaɓa ya samu kujerar shugabancin jam’iyyar.

‘Yan takara 6 ne su ka janye masa kafin a fara babban taron, inda Sanata Musa, ɗaya daga cikin su ya bayyana cewa mataki mai matuƙar wahala.
A wata takarda mai shafi 12 wanda aka raba a farkon taron, gwamnoni 22 na jam’iyyar sun bayyana mutum 78 domin samun kujeru a jam’iyyar.

Jerin sunayen waɗanda sauyin ya ritsa da su
Waɗanda abinda gwamnoni su ka yi ya ritsa da su sun haɗa da:

  1. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani
  2. Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Adamu Aliyu
  3. Injiniya Ife Oyedele
  4. Architect Waziri Bulama
    Mutanen huɗu su na neman kujerun mataimakin shugaban jam’iyya (yankin kud), mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa (yankin arewa), magatardan jam’iyya na ƙasa da kuma shugaban tsare-tsare.

A madadin su, gwamnonin sun zaɓi, Chief Emma Enuekwu, Sanata Abubakar Kyari, Sanata Iyiola Omisore, da kuma Suleiman M. Argungu.
Cire mutanen guda huɗu ya tabbatar da labarin Daily Trust na ranar Laraba akan ƙulla-ƙullar da gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar ke yi wajen tsame ‘yan takarar da shugaba Buhari ke goyon bayan su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe