24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Yawan kashe-kashe ya sa an saba da jimamin mutuwa a jihar Kaduna, CAN

LabaraiYawan kashe-kashe ya sa an saba da jimamin mutuwa a jihar Kaduna, CAN

Ƙungiyar Christian Association of Nigeria (CAN) reshen jihar Kaduna ta miƙa ta’aziyyar ta kan waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya ritsa da su a daren ranar Litinin. Jaridar Leadership ta rahoto

CAN ta koka kan yawaitar kashe-kashe a jihar Kaduna

CAN ta bayyana cewa zaman makoki ya zama ruwan dare a jihar Ƙaduna saboda yawan hare-hare da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi a jihar.


CAN
Shugaban ƙuNgiyar CAN reshen jihar Kaduna, John Joseph Hayab. Hoto daga jaridar The Cable

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Rev. John Joseph Hayab, ya fitar, ya bayyana cewa:

Abin baƙin ciki, zaman makoki ya zama ruwan dare a jihar Kaduna duk da cewa muna da gwamnati wacce ake ba kuɗaɗen tsaro kowane wata. Bayan haka, harin jirgin ƙasan ya bayyana raunin da mutanen jihar Kaduna da duk wani mai kasuwanci a jihar ke fuskanta saboda ƙaruwar ta’addanci.

CAN da duk wasu ma su ruwa da tsaki sun koka kan yadda mutanen jihar Kaduna da baƙi ma su shigowa a bangaren musulmai da kiristoci ke rayuwa cikin ɗar-ɗar a kowane lokaci saboda yadda ‘yan bindiga su ka nuna sun fi ƙarfin gwamnatin da mu ke da ita. A cewar sa.

Ƙungiyar ta yi wani muhummin kira ga gwamnatin tarayya

CAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi iyakar bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta murƙushe ‘yan bindiga ma su cin karen su ba babbaka a jihar Kaduna da wasu sassa na Najeriya domin kawo ƙarshen raɗaɗin ɓakin cikin waɗanda abin ke ritsa wa da su.

Harin Jirgin kasa Daga Abuja zuwa Kaduna:Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka-Amaechi

Ministan sufuri Amaechi wanda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci wurin da harin ya faru, ya ce za a iya kaucewa faruwar wannan lamarin da ace an samu na’urar tsaro ta dijital ta kimanin Naira biliyan 3.

Ya ce yanzu sai an kashe sama da Naira biliyan 3 don gyare gyaren abubuwan da aka yi hasara yayin da aka harin hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Mun san daga ina matsalar ta ke. Muna da buƙatar samun kayan tsaro na dijital.

Saboda da ace muna da waɗannan kayan aikin, ba za ku ga kowa a kan wannan hanyar ba. Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka. Yanzu, gashi abinda ya faru, Mutane takwas sun rasa ransu, mutane 25 sun jikkata suna kwance a asibiti,Mutanen da aka sace bamu san adadin su ba , kudin kayan aikin da za a sa wannan digital din Naira biliyan uku ne kacal. Gashi yanzu anyi asarar abin da ya haura Naira biliyan uku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe