35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ba zai yiwu inyi Shagalin bikin zagayowar ranar haihuwa ta ba Ana tsaka da jimami-Tinubu

LabaraiBa zai yiwu inyi Shagalin bikin zagayowar ranar haihuwa ta ba Ana tsaka da jimami-Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu @70
Ba zai yiwu inyi Shagalin bikin zagayowar ranar haihuwa ta ba Ana tsaka da jimami-

Baki daga ko ina a fadin kasar sun halarci taron shagalin bikin zagayowar haihuwar Tinubu

An shirya ko ina baƙi waɗanda suka taho daga nesa da kusa suna zaune cikin farin ciki, da annashuwa.

Taron ya fara gudana inda aka gabatar da wasu daga cikin manyan baki. Wasu kuma suna hanyar su ta isowa babban filin taro na Eko Hotel, Victoria Island, Legas, wurin da za a gudanar da shagalin.
Ana tsaka da shagali sai aka samu sanarwar cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, uban gayya ya sami kira.

Tinubu ya bayyana jimamin sa game da harin jirgin kasa da aka kai a hanyar kaduna zuwa Abuja

Wuri ya dauki shiru ana sauraro. Kwatsam sai akaji mummuna labari.

Tinubu ya bayyana cewa taron bikin cikar shekaru 70 da haihuwar ya sami tsaiko saboda harin ta’addancin da aka kai kan titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna inda mutane 8 suka mutu, 29 suka jikkata tare da sace wasu da dama.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya ce: “Ya kamata a ce yau rana ce ta farin ciki saboda na cika shekaru 70 a duniya. Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu ikon yin rayuwa har zuwa wannan lokaci.
Yanzu nan nasami wani labari mai ban tausayi da ya faru a kasar nan, abin takaici ne yadda aka kashe mutane sama da 60 a cikin jirgin kasa tsakanin Kaduna da Abuja a daren jiya.

Wannan lamari ne mai matukar muni game da tsaron rayuka a kasar nan kuma yana kira da a ayi dubi ga wannan lamari.

Inzo nan ina murna, ina raye-raye da jin daɗi idan nayi haka ban zama cikakken mai kishi kasa ba da nuna damuwa ga kasa ta ba.

Ina kira ga malamai da su ci gaba da addu’a kuma kowa ya koma ya cigaba da addu’a.

Bai kamata a gudanar da wannan taron ba. Na tattauna da manyan mutane kuma sun yarda da ni. Na kasance mai kishin dimokradiyya; Na aminta da shawarar su cewa a soke wannan taron bikin.

Muna addu’a ga rayukan da suka rigamu gidan gaskia Allah ya jikan su. Muna kuma rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya taimake mu Ya sa mu ci nasara a kan wadannan miyagun ayyuka, Ya dora Nijeriya a kan tafarki madaidaici, Ya albarkace mu, Ya kuma yi mana jagora a dukkan abinda muke yi.

Ina so mu yi shiru na minti daya domin jimami ga wannan bala’i da ta afku. Allah Ta’ala Ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu, ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma ba wadanda suka jikkata lafiya.”

Kafin a soke taron shagali, bugu na 13 mai taken: ‘Sanya Nijeriya cikin sabuwar tsarin duniya: Mahimmancin shugabanci na gari, babban bako malami, Farfesa Olufemi Bamiro, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ibadan, da sauran wadanda zasu gabatar da jawabi a wannan taro duk sun iso.

Taron ya sami halaryar manyan Baki

Cikin wadanda suka iso wurin sun hada da mai masaukin baki Gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Dr. Obafemi Hamzat da sauran manyan baki da suka hada da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola, mataimakin gwamnan jihar Osun Benedict Alabi, da wakilin sakataren gwamnatin tarayya Andrew Adejo, Sakataren APC na kasa Sanata Iyiola Omisore, Cif Bisi Akande, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Osemawe na Ondo, Oba Victor Kiladejo, Deji na Akure, Oba Adelusi Aladetoyinbo da Olugbo na Ugboland, Oba Fredrick Akinruntan, da kuma Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero duk sun iso wurin taron.

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, uwargidan gwamnan jihar Legas, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, Sanata Abu Ibrahim, tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja, Musa Ibeto, Sanata Kashim Shettima, T.A. Gwazo, Sanata Ibikunle Amosun, hamshakin dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote, Mista Femi Otedola, Sanata Tokunbo Abiru da Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi duk sun sami halarta.

Tinubu ya isa filin taron ne da misalin karfe 2:42 na rana cikin murna da jin dadi.

Yadda na sha da ƙyar a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, Rahama Sadau
Shahararriyar jarumar fina-finan Najeriya, Rahama Sadau tare da iyalan ta sun godewa Allah bayan da jarumar ta wallafa yadda ta samu ta tsira daga harin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja. Jaridar Daily Trust ta rahoto

An kai ma jirgin ƙasan hari
A daren ranar Litinin, ‘yan ta’adda sun kai hari ga jirgin ƙasan kan hanyar sa ta zuwa Kaduna. Sun saka bam a hanyar jirgin wanda hakan ya sanya dole jirgin ya tsaya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan daga baya sun zagaye kusan ilahirin jirgin sannan su ka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya janyo mutane da dama su ka rasa ran su.
A wata wallafa da ta yi a shafin ta na Instagram, jarumar ta bayyana cewa ita da ƙanwar ta sun shirya shiga jirgin amma sai jirgin ya tafi ya bar su. Sai dai ta bayyana cewa akwai ƙawayen ta waɗanda harin ya ritsa da su a cikin jirgin.

Ta rubuta cewa:

“Ni da ƙanwata mun shirya bin jirgin da aka kai wa hari amma mun rasa shi. Da ya kasance da ni da ƙanwata abin ya ritsa da su amma mu duka ne.. Muna da ‘yan’uwa da abokan arziƙi a cikin jirgin. Yaushe zaa kawo ƙarshen wannan abin.
Jarumar kuma ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga masoyan ta da su tabbatar cewa sun samu katin zaɓen su sannan kuma su tsare ƙuri’un su.

Rahama Sadau ta bayyana cewa:

Abin zai cigaba da muni ne yayin da zaɓe ya ke ƙaratowa kuma arewa ce zaa yi ta hari. Ina gaya mu ku cewa ku yi katin zaɓe sannan ku ƙada ƙuri’un ku amma wa za ku zaɓa? Irin mutanen da ke kan mulki a yanzu??? Dan Allah ku yi katin zaɓe.
Mu ‘yan arewa mu ne mu ka janyowa kan mu wannan bala’in, mun zaɓi da a ƙuntata mana saboda mu na tsoro. Kuma mun ƙasa fahimtar cewa akwai ƙarfin ikon a hannun mu.. Ba mu son yarda da cewa shugabannin mu sun ba mu kunya kuma tabbas sun ba mu!!!

Yawan jami’an tsaron da na gani yau a filin wasa na MKO Abiola, na fahimci cewa Najeriya za ta iyayin duk abinda ta ke son yi, amma sun zaɓi da su kyale kashe-kashen da kuma gabaɗaya fannin tsaro.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe