35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Harin Jirgin kasa Daga Abuja zuwa Kaduna:Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka-Amaechi

LabaraiHarin Jirgin kasa Daga Abuja zuwa Kaduna:Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka-Amaechi
hqdefault

Amaechi ya bayyana alhinin sa game da faruwar harin titin jirgin kasa da aka kai

Ministan sufuri Amaechi wanda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci wurin da harin ya faru, ya ce za a iya kaucewa faruwar wannan lamarin da ace an samu na’urar tsaro ta dijital ta kimanin Naira biliyan 3.
Ya ce yanzu sai an kashe sama da Naira biliyan 3 don gyare gyaren abubuwan da aka yi hasara yayin da aka harin hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Mun san daga ina matsalar ta ke. Muna da buƙatar samun kayan tsaro na dijital.

Karamin aiki ya ja babba hasara

“Saboda da ace muna da waɗannan kayan aikin, ba za ku ga kowa a kan wannan hanyar ba. Sai da nayi gargadin cewa za a iya rasa rayuka. Yanzu, gashi abinda ya faru, Mutane takwas sun rasa ransu, mutane 25 sun jikkata suna kwance a asibiti,Mutanen da aka sace bamu san adadin su ba , kudin kayan aikin da za a sa wannan digital din Naira biliyan uku ne kacal. Gashi yanzu anyi asarar abin da ya haura Naira biliyan uku.gashi an la’anta hanyoyin jirgin mun rasa abin hawa da masu horar da matuka jirgin. Mun yi hasarar mutane, Kuma kayan aikin bai fi karfin mu ba Naira biliyan uku ne kawai.
“a yanzu sai an kashe sama da Biliyan uku domin gyaran abubuwan da aka rasa a yanzu, zai kashe mu fiye da Naira biliyan 3. Kuma a halin da ake ciki a yanzu ko an bamu izinin saya zai bada wahala a da dala N400, yanzu ta koma N500. In kace zakayi gaskiya a gwamnati mutanen da kake tare da su suna kawo maka cikas,dole kaji bakin cik
i.

Jerin Sunaye:Amurka ta fallasa jerin sunayen ‘yan Najeriya 6 dake daukar nauyin Boko Haram
A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya fitar, ‘yan Najeriyar da aka sanyawa takunkumin sun yi “wajen taimakawa, da daukar nauyi, ko bayar da tallafin kudi, kayan aiki, fasahar kere-kere, kayayyaki ko ayyuka ga kungiyar Boko Haram.

Ga Jerin sunayen:

Abdurrahman Ado Musa
Salihu Yusuf Adamu
Bashir Ali Yusuf
Bashir Ali Yusuf
Muhammed Ibrahim Isa
Ibrahim Ali Alhassan Surajo
Abubakar Muhammad
‘Yan Najeriyar da aka sanya wa takunkumi an yanke musu hukunci ne tun a Dubai
A cikin sanarwar an bayyana matakin da Amurka ta dauka ya biyo bayan tuhumar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi na yanke hukunci, da kuma bayyana sunayen ‘yan Najeriya da aka lissafa wadanda ake tuhumar su da laifin tallafawa ta’addanci.
Labarun Hausa ta kuma ruwaito cewa, tun da farko wata kotun daukaka kara dake birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wannan hukuncin. Inda Ake tuhumar su da laifin tallafawa kungiyar Boko Haram ta hanyar ba da damar aika kudade daga Dubai zuwa Najeriya domin kara ta’azzara ta’addanci.

Biyu daga cikin su an yanke musu hukuncin rai da rai
Biyu daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu, an yanke musu hukuncin daurin rai da rai. Sauran hudun da suka hada da: Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe