24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Yadda na sha da ƙyar a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, Rahama Sadau

LabaraiKannywoodYadda na sha da ƙyar a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, Rahama Sadau

Shahararriyar jarumar fina-finan Najeriya, Rahama Sadau tare da iyalan ta sun godewa Allah bayan da jarumar ta wallafa yadda ta samu ta tsira daga harin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja. Jaridar Daily Trust ta rahoto

An kai ma jirgin ƙasan hari

A daren ranar Litinin, ‘yan ta’adda sun kai hari ga jirgin ƙasan kan hanyar sa ta zuwa Kaduna. Sun saka bam a hanyar jirgin wanda hakan ya sanya dole jirgin ya tsaya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan daga baya sun zagaye kusan ilahirin jirgin sannan su ka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya janyo mutane da dama su ka rasa ran su.

Rahama Sadau ta bayyana yadda ta tsira daga harin jirgin

A wata wallafa da ta yi a shafin ta na Instagram, jarumar ta bayyana cewa ita da ƙanwar ta sun shirya shiga jirgin amma sai jirgin ya tafi ya bar su. Sai dai ta bayyana cewa akwai ƙawayen ta waɗanda harin ya ritsa da su a cikin jirgin.

Ta rubuta cewa:

“Ni da ƙanwata mun shirya bin jirgin da aka kai wa hari amma mun rasa shi. Da ya kasance da ni da ƙanwata abin ya ritsa da su amma mu duka ne.. Muna da ‘yan’uwa da abokan arziƙi a cikin jirgin. Yaushe zaa kawo ƙarshen wannan abin.

Rahama Sadau
Yadda na sha da kyar a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, Rahama Sadau

Ta yi wani muhimmin kira ga masoyan ta

Jarumar kuma ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga masoyan ta da su tabbatar cewa sun samu katin zaɓen su sannan kuma su tsare ƙuri’un su.

Rahama Sadau ta bayyana cewa:

Abin zai cigaba da muni ne yayin da zaɓe ya ke ƙaratowa kuma arewa ce zaa yi ta hari. Ina gaya mu ku cewa ku yi katin zaɓe sannan ku ƙada ƙuri’un ku amma wa za ku zaɓa? Irin mutanen da ke kan mulki a yanzu??? Dan Allah ku yi katin zaɓe.

Mu ‘yan arewa mu ne mu ka janyowa kan mu wannan bala’in, mun zaɓi da a ƙuntata mana saboda mu na tsoro. Kuma mun ƙasa fahimtar cewa akwai ƙarfin ikon a hannun mu.. Ba mu son yarda da cewa shugabannin mu sun ba mu kunya kuma tabbas sun ba mu!!!

Yawan jami’an tsaron da na gani yau a filin wasa na MKO Abiola, na fahimci cewa Najeriya za ta iyayin duk abinda ta ke son yi, amma sun zaɓi da su kyale kashe-kashen da kuma gabaɗaya fannin tsaro.

Rahama Sadau: Ba zan iya barin sana’ar fim ba saboda aure

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau ta ce ba za ta taba iya barin harkar fim ba saboda aure. Ta fadi hakan ne a wata tattaunawa da tayi da mabiyanta a ranar Laraba a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A tattaunawar ta mintuna 30 da jarumar tayi da mabiyanta na kafar sada zumuntar, inda suka yi ta tambayarta akan rayuwarta, wani mabiyinta ya tambayeta idan za ta iya sakin harkar fim don tayi aure. Amma a amsar da Sadau ta ba shi, mamaki tayi akan yadda mata da dama suke sana’o’insu amma ake caccakar harkar fim.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe