24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wata mata ta haifi jariri mai ido ɗaya a ƙasar Yemen

LabaraiWata mata ta haifi jariri mai ido ɗaya a ƙasar Yemen

Wata mata ta haifi wani jariri mai ido ɗaya kawai a asibitin Al Hilal Medical Hospital a birnin Al-Bayda, na ƙasar Yemen.

Wani ɗan jarida a ƙasar Yemen, Karim Zarari, ya rahoto cewa an haifi yaron ne da kurmin ido ɗaya da ƙwayar ido ɗaya.  Karim Zarari ya kuma wallafa hotunan jaririn.

Mutumin da ke a cikin hoton wani likita ne mai aiki a asibitin mai suna, Munif Hatem bin Shihab Al-Din.

Ba kasafai ake samun irin wannan lamarin ba

Zarari yayi sharhin cewa lamarin wannan jaririn abu ne wanda ba kasafai ya ke faruwa ba.

A cewar likitoci, akwai rami a cikin idon jaririn sannan yana da jijiya ɗaya kawai ta gani. Sau shida kawai aka taɓa samun irin wannan a cikin ƙarni biyar da su ka gabata a duniyar nan.

Mutane na tunanin an haifo Dajjal

Mutane sun nuna damuwar su kan cewa ko an haifi Dajjal ne. Inda su ka yi imanin cewa Dajjal zai zo ne yana mai ido ɗaya.

Sai dai, magana ta gaskiya ita ce, kamar yadda addinin musulunci ya nuna, Dajjal makaho ne mai ido ɗaya. Yana da kwayar ido biyu amma ba zai iya gani da ɗaya daga cikin su ba.

Wane hali jaririn ya ke ciki

Jaririn ya rayu ne na tsawon sa’o’i bakwai kacal a duniya kafin nan ya rasu. Hukumomin lafiya na ƙasar Yemen har yanzu ba su ce komai ba akan wannan lamarin.

Allahu Akbar: Bidiyon dokin da wata mata ta haifa a garin Zaria

A duk lokacin da aka kira Allah, Ubangiji mahalicci, dole mutum ya yarda da cewa shi ne mai yin komai da kuma kowa.

A ranar Talata, 21 ga watan Maris na shekarar 2022 da yamma labarin yadda wata mata ta haifi wata halitta mai kama da doki ya bazu a garin Zaria cikin Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a layin Lemu da ke Tudun wadan Zaria kamar yadda ganau suka shaida wa wakilin Labarun Hausa.

Bayan isa gidan da lamarin mai ban al’ajabi ya faru, wakilin Labarun Hausa bai samu damar ganawa da matar da ta haifi jaririn dokin ba, amma ya gan ta kuma makwabtan ta sun tabbatar masa da hakan.

Source: Lifeinsaudiarabia

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe