24.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Wani tsohon mataimakin ciyama ya rabauta da hukuncin zaman gidan yari har na shekara 12 sakamakon almundahana

LabaraiWani tsohon mataimakin ciyama ya rabauta da hukuncin zaman gidan yari har na shekara 12 sakamakon almundahana

An yankewa tsohon mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna Hassan Dauda, hukuncin shekara 12 a gidan gyaran hali, sakamakon sa hannun sa a badakalar Naira miliyan N6.3m na aikin Hajji. 


Dauda din wanda hukumar ICPC ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar Kaduna, ana zargin sa ne da damfarar mutane 7 kudi kimanin Naira miliyan N6, 342,000. 


Hukumar ta ICPC din tana zargin sa, da tuhumomi daban-daban har 16, wanda suka hada da, bayyana kansa a matsayin wanda ba shiba, amfani da mukamin ofishi domin almundahana, da kuma shirya takardun bogi. 

Wani tsohon mataimakin ciyama ya rabauta da hukuncin zaman gidan yari har na shekara 12 sakamakon almundahana
Wani tsohon mataimakin ciyama ya rabauta da hukuncin zaman gidan yari har na shekara 12 sakamakon almundahana

Tuhumomin da mai shriah ya yiwa mataimakin ciyama na bogi


Mai sharia M. T Aliyu, yan tuhumar Dauda din da amfani da mukamin mai taimakawa shugaban karamar hukumar Giwa, domin ya damfari mutanen da basuyi tsammanin karya yake yi ba, da sunan zai sama musu kujerun aikin Hajji a shekarar 2013, laifin da ya cancanci hukunci a karkashin sashi na 19 na kundin hukumar ICPC din na shekarar 2000.


Da yake yanke hukuncin, mai sharia Aliyu, kamar yadda aka zayyana, na laifin sojan gona, ya kamashi da laifi, kuma ya yanke masa hukuncin shekara 7 a gidan gyaran hali, ba tare da zabin tara ba. 


A bangaren laifin bata aiki  ofis kuwa, da aka sake tuhumar sa, an yanke masa shekara 5 ba tare da zabin tara ba. 
A tuhumar takaddar bugi kuwa kotu ta wanke shi. 


Da yake karanta hukuncin, mai shariar, ya bayyana cewa hukumar ICPC din zata iya karbar hukuncin ba tare da wani shakku ba, kuma mai laifin zai share wa’adin sa ne a hade ba rarrabe ba. 


Idan za’a iya tunawa, jami’an hukumar ICPC sun kama mai laifin ne a watan Oktoban 2013, bayan karar zargin damfara da rashawa, inda aka cafke shi a watan Mayu na shekarar 2015,  bayan kammala bincike.

Tsufa ya zo da gardama: Kotu ta gurfanar da tsohon da ya tafka damfarar N20.7m

An gurfanar da wani dattijo Fasasi Adebambo, a gaban wata babbar kotun Legas jiya bisa laifin damfarar naira miliyan N20.7 (N20.7m)

An miƙa dattijon gaban alƙali

Adebambo, mai shekaru 84, an miƙa shi gaban alƙaliwa Akintayo Aluko tare da wani Ojobaro Kayode bisa zargin aikata zamba cikin aminci. Jaridar The Nation ta rahoto


Sashin ‘yan sanda na Police Special Fraud Unit (PSFU), wanda ya miƙa waɗanda ake zargin, ya tuhume su da cewa sun amshi kuɗaɗen ne a wajen Dr. Mbeledogu da matarsa akan cewa za su sayar musu da wani gida a yankin Maryland a jihar Legas.

Mai shigar da ƙara na PSFU, Henry Obiaze, ya faɗawa kotu cewa waɗanda ake zargin sun tafka wannan aika-aikar ne tsakanin watan Janairu da Fabrairun 2020.

Ya bayyanawa kotu cewa laifukan da su ka aikata sun saɓawa sashin doka na 8 (a) da 1(1)(a) na hana aikata damfara da sauran laifuka makamantan su na shekarar 2006. Sannan kuma abin hukuntawa ne a sashi na 3 na cikin dokar.

Sun ƙi amsa aikata laifin

Waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Bayan sun musanta aikata laifukan, mai shigar da ƙara ya nemi kotu da ta sanya ranar fara shari’a sannan ya buƙaci kotu da ta sakaya su a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

Kano: Yadda kotu ta sakaya Ado a gidan yari akan satar dunkulen Maggi

Wata kotu da ke zama a Jihar Kano ta sakaya wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali akan satar katan din dunkulen maggi, LIB ta ruwaito.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

https://youtube.com/watch?v=HbCdlCh0R74%3Ffeature%3Doembed

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe